A wannan makon, ƙungiyar ECOWAS za ta yi bikin cika shekaru 50 da kafuwa.
An kafa ƙungiyar ne a ranar 28 ga watan Mayu, 1975 a birnin Legas da ke Nijeriya, da nufin inganta tattalin arziƙi, haɗin gwiwa da kuma tsaro tsakanin kasashen Yammacin Afrika.
- Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [17]
- Kamfanin Apple Ya Sanar Da Zuba Sabon Jari A Fannin Samar Da Makamashi Mai Tsafta A Sin
Ƙasashen da suka kafa ECOWAS sun haÉ—a da Benin, Burkina Faso, Côte d’Ivoire, Gambia, Ghana, Guinea, Guinea-Bissau, Liberia, Mali, Mauritania, Nijar, Nijeriya, Senegal, Saliyo, da Togo.
Daga baya, a 1977, ƙasar Cape Verde ta shiga cikin ƙungiyar, amma Mauritania ta fice a shekarun 1999 zuwa 2000.
A shekarar 1990, ECOWAS ta kafa rundunar ECOMOG domin tabbatar da zaman lafiya a wasu ƙasashen da ke fama da rikici.
Wannan ya taimaka wajen kawo ƙarshen yaƙin basasa a Laberiya da Saliyo.
Duk da haka, ƙungiyar ta fuskanci ƙalubale, musamman bayan juyin mulki a ƙasashen Mali, Burkina Faso, da Nijar a cikin shekarun baya-bayan nan.
Shin ECOWAS na iya ci gaba da aiwatar da ayyukanta kamar da?
Sai dai har yanzu wasu na yi wa ƙungiyar kallon hadarin kaji, kan zargin ta gaza cimma wasu muradu da aka kafa ta a kai.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp