Hukumomi biyu da suke yaki da cin hanci da rashawa da dangoginsu wato EFCC da ICPC, sun samu nasarar kwato naira biliyan 277.685 da kuma kudin da yawansa ya kai dala miliyan 105,966 a cikin shekara daya.
Yayin da EFCC ta kwato rukunin gidaje 753, ita kuma ICPC ta bi diddingin ayyuka 1,500 a fadin kasar nan.
- Gwamna Lawal Ya Rattaba Hannu Kan Kasafin Kudi Na Naira Biliyan 546 Na Shekarar 2025
- Yadda Minista Ya Kaddamar Da Ginin Radio House Da Aka Yi Wa Kwaskwarima A Abuja
Kazalika, ICPC ta samu nasarar dakile ma’aikatu da sashi-sashi daga taba naira biliyan 10.8 na kudaden da ba a yi amfani da su ba.
Hukumomi biyun sun samu nasarar gurfanar da mutane 3,468 da laifuka daban-daban a cikin shekara guda.
Daraktan sashin shari’a na ofishin mashawarcin shugaban kasa kan harkokin tsaro (ONSA), Zakari Mijinyawa, shi ne ya shaida hakan a hirarsa da ‘yan jarida a Abuja jiya.
Mijinyawa ya ce a halin yanzu tsofaffin gwamnoni hudu da tsofaffin ministoci uku su na kan fuskar shari’a a kotuna daban-daban. Sai dai bai bayyana sunayen su ba.
Ya misalta nasarorin hukumomin biyu a matsayin wata gagarumar ci gaba da kokarin gwamnati na yaki da cin hanci da rashawa a fadin kasar nan.
“A karkashin jagorancin babban shugaba, Ola Olukoyede, EFCC ta aiwatar da sauye-sauye masu gayar ma’ana, da suka hada da kafa sabuwar sashi-sashi na yaki da ‘yan damfara, farfado da ofisoshin shiyyoyi, da kuma kafa gidan rediyon EFCC 97.3FM domin wayar da kan jama’a.
‘’Hukumar ta amshi bakwancin babban taro kan laifukan yanar gizo da masu ruwa da tsaki ciki har da Shugaba Bola Ahmed Tinubu suka halarta.
“Hukumar ta sashin tawagar musamman dinta ta samu nasarar gurfanar da masu laifukan 35 da suka ci zarafin Naira.
‘’A duniyance, EFCC ta samu inganta hadaka da FBI da Canadian Royal Mounted Police, da kwato kadarorin da aka boye a kasashen waje.”
Ya ce gurfanar da tsofaffin gwamnoni da ministoci ciki har da tsohon gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, kan sama da fadi da duniyar al’umma da sauran laifuka ya nuna kokarin hukumar wajen wanzar da gaskiya da adalci.
Ya ce, “Nasarorin da ICPC ya cimma a 2024 abun alfahari ne. Hukumar ta kwato tsabar kudi na naira biliyan 29.685 da dala 966,900.83, da kuma kari kan dakile ma’aikatu da sashi-sashi daga taba naira biliyan 10.8 na kudaden da ba a yi amfani da su ba.