Hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) reshen shiyyar Illorin a ranar Asabar ta samu nasarar cafke wasu mutum bakwai bisa zarginsu da damfara ta yanar gizo a Illorin da ke jihar Kwara.
mutum biyu cikinsu malaman addini ne da suka hada, Ahmed Abdulkadir da kuma Abdullateef Ajibola, da ake zargin suna hada kai domin yin tsafin neman nasara ga sauran abokan cin burminsu masu damfara a yanar gizo.
- NDLEA Ta Cafke Tsohon Sojan Da Ke Wa ‘Yan Bindiga Safarar Miyagun Kwayoyi
- Damfarar Miliyan 66: Kotu Ta Daure Maman Boko Haram Da Wasu Mutum 2
Sauran dai su ne Tomiwa Kingsley, wani dan yi wa kasa hidima da ke sabis a karamar hukumar Patigi a jihar; Mujeeb Jatto da Adebayo Sofiullah da kuma Okeke Wisdom sai Festus Ogeleka.
Hukumar ta EFCC ta ce binciken farko-farko ya gano cewa Malaman biyu sun kama daki a wani otel a Illorin domin yin tsafin neman nasara ga sauran wadanda aka cafke kan wannan zargin.
Hukumar ta ce wadanda ta kaman suna taimaka mata da bayanan da suka dace a binciken da ake musu, kana zata gurfanar da su a gaban kotun da zarar masu bincike suka kammala aikinsu.