A ranar Talata, jami’an shiyyar Maiduguri na Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC) sun kama manyan motoci 21 da ke dauke da kayan abinci da ke kan hanyarsu ta zuwa wasu kasashe makwabta.
A wata sanarwa da ya fitar, Jami’in hulda da jama’a na hukumar ta EFCC, Mista Dele Oyewale, ya ce an kama motocin ne a wani samame da suka kai a wasu manyan hanyoyin fita da ke kan titin Kalabiri/Gamboru Ngala da Bama, a Jihar Borno.
Oyewale ya ce binciken da aka yi ya nuna cewa an boye kayan abincin da wayo a cikin manyan motocin da aka yi musu bad da kama, amma da yake jami’an EFCC suna da lura sai suka gano su.
Ya kuma kara da cewa, takardun kayan sun nuna cewa za a kai su N’djamena, da ke Jamhuriyar Chadi, da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya da kuma Kamaru.
“Ana sa ran kame manyan motocin zai kawo karshen matsalar karancin abinci da marasa kishin kasa ke fasa-kwauri a fadin kasar nan,” in ji Oyewale.
Kakakin hukumar ta EFCC ya kara da cewa da zarar an kammala binciken da ya kamata za a gurfanar da masu laifin a gaban kotu.