Hukumar yaki da ci hanci da rashawa (EFCC) ta gayyaci tsohon ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika domin bincike kan aikin samar da Jirgin Nijeriya a karkashin kamfanin ‘Nigeria Air’.
Ministan zai iya bayyana a gaban hukumar a cikin makon nan domin amsa tambayoyi kan kaddamar da Jirgin Nijeriya da kuma zargin kashe naira biliyan 3 wa shirin samar da Jirgin Nijeriya.
Kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar da cewa akwai binciken fa suke cigaba da yi kan zargin da ke makale ga aikin samar da Jirgin Nijeriya, samma bai bada cikakken bayani kan hakan ba.
Ya ce, “Zan iya tabbatar muku cewa akwai binciken da ake kan yi kan wannan batun.”
Wasu majiyoyi daga EFCC sun ce, hukumar za ta bincike naira biliyan uku da suke yi bace bat da sunan aikin.
Tunin dai EFCC ta gudanar da tambayoyi kan wasu jami’an kamfanin Nigerian Air kan kaddamar da Jirgin Nijeriya da aka yi a kwanakin baya a Abuja.
Idan za a iya tunawa dai, Hadi Sirika a kwanakin baya ya shaida a wata gidan Talebijin cewa Gwamnatin tarayya ta kashe naira biliyan uku wajen aikin kamfanin Nigeria Air zuwa yanzu.
Tsohon ministan da yake bayani a Arise News Channel ranar Lahadi, ya ce, an yi kasafin aikin zai lakume biliyan biyar a shekaru bakwai da suka wuce, amma biliyan uku ne kawai aka fitar.
Kazalika idan za ku tuna, kafin saukar Gwamnatin shugaba Buhari ‘yan kwanaki kalilan, ministan ya gabatar da wata jirgi da aka yi zargin mallakin Habasha ce wato Ethiopian inda aka kaddamar a Nijeriya dauke da zanen tambarin Nijeriya.
Mutane da dama sun dauka Jirgin mallakin Nijeriya ne amma daga baya shugaban kamfanin Nigeria Air ya fito ya ce Jirgin hayarsa aka dauko ba na Nijeriya ba ne.