Shugaban Kasa, Bola Tinubu, ya bukaci Gwamnonin Nijeriya da su yi aiki tukuru domin gudanar da shugabanci na kwarai ga al’ummar su.
Ya yi wannan bukatar ne a ranar Alhamis sa’ilin nan da ke kaddamar da Majalisar Tattalin Arzikin Kasa (NEC), wanda mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ke jagoranta.
Dukkanin Gwamnonin Nijeriya su 36 tare da sauran Jami’ai ne suka kasance mambobin Majalisar.
Tinubu ya ce, Gwamnoni ba su ma da uzurin da za su gabatar wajen kasa-kasau ko rashin nasara duk da roko, rokon a zabesu, har ma da rawar da suka taka domin a zabesu a lokacin yakin zaben 2023.
A cewarsa, ‘yan Nijeriya na bukatar a farfado da tattalin arziki cikin gaggawa, don haka akwai bukatar su hada hannu da Gwamnonin wajen cimma wannan nasarar.
Shugaban ya nemi Majalisar da ta hada karfi da karfe da gwamnatinsa domin cimma nasarori kan farfado da tattalin arzikin kasar nan cikin kankanin lokaci.
Bayan kaddamar da Majalisar, mambobin Majalisar sun shiga ganawa ta farko a fadar shugaban kasa da ke Villa, Abuja.
LEADERSHIP ta labarto cewa, NEC din na da alhakin bada shawarori wa shugaban kasa dangane da lamuran da suka shafi harkokin tattalin arzikin kasa da matakan da za a dauka wajen tsara hanyoyin da shirye-shiryen tafiyar da tattalin arziki na gwamnatoci da na tarayya.
Mambobin kwamitin sun hada da Gwamnonin Nijeriya su 36, gwamnan babban Bankin kasa (CBN) da kuma wasu jami’an gwamnati da aka shigo da su.
Daga cikin wadanda suka halarci taron ganawar Majalisar Tattalin Arzikin Kasa NEC a lokacin da aka fara sun hada Gwamnonin jihohin Kwara Abdulrahman Abdulrazaq; Osun, Ademola Adeleke; Kogi, Yahaya Bello; Ekiti, Biodun Oyebanji; Nasarawa, Abdullahi Sule; Akwa Ibom, Umo Eno, da kuma na jihar Enugu, Peter Mbah.
Sauran sun hada da Gwamnonin jihohin Cross River, Bassey Otu; Plateau, Caleb Mutfwang; Kebbi, Nasir Idris; Katsina, Umar Dikko Radda, da gwamnan Jihar Benue Hycinth Alia.
Kazalika a wajen ganawar akwai Gwamnonin Zamfara, Dauda Lawal; Ogun, Dapo Abiodun; Anambra, Charles Soludo; Yobe, Mai Mala Buni; Taraba, Agbu Kefas; Gombe State, Inuwa Yahaya; Delta, Sheriff Oborevwori; Rivers, Siminalayi Fubara; Niger, Mohammed Bago, da na jihar Sokoto, Ahmed Aliyu.
Saura sun hada da: Ebonyi, Francis Nwifuru; Kaduna, Uba Sani; Edo State, Godwin Obaseki; Abia, Alex Otti; Bayelsa, Douye Diri; Kano, Abba Yusuf; Bauchi, Bala Mohammed; Oyo, Seyi Makinde; da mai rikon mukamin gwamnan Jihar Ondo, Lucky Ayedatiwa, da kuma mataimakin Gwamnan Jihar Borno Borno, Umar Kadafur.
Sakataren Gwamnatin tarayya, George Akume; shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila; babban jami’in gudanarwa (GCEO) na kamfanin albarkatun Mai Mai kasa (NNPCL), Mele Kyari; mukaddashin Akanta-janar na tarayya, Oluwatoyin Madein; mukaddashin gwamnan CBN, Folashodun Shonubi; manyan sakatarorin ma’aikatar kasafi da tsare-tsaren tattalin arzikin, na birnin tarayya (FCTA) da na fadar shugaban kasa duk sun halarci taron ganawar Majalisar Tattalin Arzikin Nijeriya.