Hukumar EFCC ta kama ‘yan ƙasar China bakwai da ‘yan Nijeriya huɗu kan haƙar ma’adinai ba tare da lasisi ba a yankin Emem-Asuk, da ke ƙaramar hukumar Eastern Obolo, Jihar Akwa Ibom.
An kama su ne yayin da suke haƙa a wani ma’adini da ake kira ilmenite (ko black sand) ba tare da izini ba.
- An Gudanar Da Taron Dandalin Tattaunawar Neman Sabon Tunani Na Asali Na 2025
- Sin: Ya Kamata A Warware Sabanin Tattalin Arziki Da Cinikayya Ta Hanyar Tattaunawa
Suna aiki a wuraren haƙo ma’adinai guda biyu da ba bisa doka ba.
Wata ɗaliba ‘yar Nijeriya da aka kama tare da su ta ce aikinta kawai fassara ne saboda tana jin harshen China.
EFCC ta ce za a gurfanar da su a kotu bayan an kammala bincike.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp