Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta kama mutane 792 da ake zargi da damfara a Jihar Legas, ciki har da ‘yan kasashen Larabawa, China, da Philippines.
Wannan shi ne mafi girman kamen da hukumar ta yi a rana guda.
- ASUU Reshen Jami’ar Sa’adu Zungur Ta Dakatar Da Yajin Aiki
- Ademola Lookman Ya Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasan Afrika Na 2024
Daraktan Hulɗa da Jama’a na EFCC, Wilson Uwajaren ne, ya bayyana haka a wani taron manema labarai da aka gudanar a ofishin hukumar da ke Legas.
A cewarsa, wadannan ‘yan damfara suna amfani da yanar gizo don cutar mutane, musamman ta hanyar yin soyayya ta karya don samun kudi daga jama’a a sassan duniya.
An kama su ne a ranar 10 ga watan Disamba a wani katafaren gida mai hawa bakwai da ke Victoria Island, a Legas.
Uwajaren, ya ce hukumar ta shafe watanni tana tattara bayanai kafin kai samamen.
Daga cikin wadanda aka kama akwai:
- ‘Yan China 148
- ‘Yan Philippines 40
- ‘Yan Khazakhtan 2
- Dan Pakistan 1
- Dan Indonesia 1
Wadannan ‘yan damfara sun dauki ‘yan Nujeriya aiki tare da biyan su sama da Naira 200,000 a kowanne wata domin taya su gudanar da ayyukansu na damfara.
An gano manyan kwamfutoci da layukan waya sama da 500 a cikin ginin, inda aka fi samun kayan aiki a hawa na biyar.
Mutanen da suka fi fadawa tarkon wadannan masu damfara sun hada da Amurkawa, ‘yan Canada, da ‘yan Mexico.
Haka nan, ‘yan damfarar suna amfani da layukan waya daga kasashen Turai kamar Jamus da Italiya don yin ayyukansu cikin sauki.