EFCC ta sake gurfanar da tsohon Gwamnan Jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed, da tsohon Kwamishinan Kuɗi, Ademola Banu, bisa sabbin tuhume-tuhume 14 kan zargin karkatar da Naira biliyan 5.78.
An gurfanar da su ne a gaban Kotun ƙolin Jihar Kwara bisa zargin karkatar da kuɗaɗen da aka ware don ayyukan jihar da samar da tsaro.
- Bikin Ranar Sikila: Yara 138,000 Ake Haihuwa Da Cutar A Duk Shekara –Dr. Kangiwa
- Hadarin Kwale-kwale A Kaiama: Gwamnan Jihar Kwara Ya Bayar Da Tallafin Naira Miliyan 100
Waɗannan tuhume-tuhume sun biyo bayan janye shari’ar da aka fara a Kotun Tarayya ta Ilorin sakamakon sauyin alƙali, bayan da aka fara shari’ar tun watan Afrilu 2024.
A cikin sabbin tuhume-tuhume, an ce tsohon gwamnan ya kashe N1.6 biliyan na tsaron jihar don hayar jiragen sama masu zaman kansu, da kuma karkatar da kuɗaɗen albashin malamai da wasu ayyukan gine-gine.
Dukkansu sun musanta tuhume-tuhumen, kuma kotu ta bayar da belinsu kan kuɗi Naira miliyan 100 tare da mutane biyu da za su tsaya musu.
Za a ci gaba da shari’ar ranar 4 da 5 ga watan Disamba, 2024.