A ranar Talata ne tsohon gwamnan Jihar Benuwe Samuel Ortom, ya amsa gayyatar Hukumar Yaki da Masu Yi Wa Tattalin Arziki Zagon Kasa (EFCC) inda ta tsare shi na tsawon sa’o’i tara.
Ortom wanda ya halarci ofishin EFCC da ke Makurdi da misalin karfe 10 na safiyar Talata.
An ruwaito cewa gwamnan ya shiga tambayoyin hukumar ne bisa zargin rashawa a cikin shekaru takwas da ya shafe na mulkin jihar.
Bayan shafe sa’o’i tara a tsare, an gano tsohon gwamnan lokacin da yake barin ofishin hukumar da misalin karfe 7:55 na dare.
Sai dai kakakin tsohon gwamnan, Terver Akase, ya ce, ba cafke Ortom hukumar ta yi, ta gayyace shi domin amsa tambayoyi.
“Tsohon gwamnan ya shafa fada cewa a shirye yake ya amsa gayyatar hukumar domin amsa tambayoyi, ya ce babu wani abin da zai boye tsawon lokacin da ya yi yana mulki.”
Sai dai EFCC ba ta fitar da wani bayani kan ziyarar da tsohon gwamnan ya kai mata ba.