Shahararren dan wasan kwallon kafa na kasar Ghana, Asamoah Gyan ya bayyana ritayarsa daga harkar kwallon kafa bayan shafe shekaru 21 a harkar.
Gyan ya yi wasanni a kungiyoyin Turai da dama ciki har da Sunderland ta Ingila, kafin ya koma Al Ain ta kasar Larabawa.
- Babu Kwamishinan Da Za A Rantsar Idan Bai Bayyana Kaddarorinsa Ba –Gwamnan Kano
- Rushewar Gini Ya Yi Ajalin Dan Shekara 15 A Neja
Gyan ya kasance babban dan wasan da kasar Ghana ke alfahari da shi tsawon rayuwar kwallonsa.
Ya buga wa Black Stars na Ghana wasanni 109 in da ya zura kwallaye 51 yayin da ya jefa shida a wasannin gasar Kofin Duniya.
Gyan ya kasance dan wasan da ya fi kowa jefa kwallaye a gasar kofin Duniya a Nahiyar Afirika, inda dan wasan Nijeriya Ahmed Musa ke biye masa da kwallo hudu.
Asamoah, ya bayyana aniyarsa ta barin kwallon kafa a wani kasaitaccen taro da hukumar wasanni ta kasar Ghana ta shirya masa domin karramawa.
Gyan ya gode wa iyali, masoya da kuma duk wani wanda ya bada gudunmuwarsa wajen ganin ya fara kuma ya gama lafiya.