Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC), ta kama tsare Tsohon Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, kan zargin almundahanar Naira biliyan 80.2.
Bello ya mika kansa ga EFCC a hedikwatarsu da ke Abuja a ranar Talata, bayan ya shafe watanni yana guje wa gayyatarsu.
- Sin: Yawan Masu Amfani Da Fasahar 5G Zai Wuce 85% A Karshen Shekarar 2027
- Cimma Burin Rage Salwantar Abinci A Kasar Sin Zai Samar Da Mafita Ga Duniya
Ya je ofishin hukumar tare da lauyoyinsa.
Kakakin EFCC, Dele Oyewale, ya tabbatar da kama shi, inda ya ce, “Yana hannunmu.”
A watan Afrilun 2024, EFCC ta ayyana Bello a matsayin wanda ta ke nema kan zargin kan almundahanar kudi.
Sai dai, a wannan karon, magajinsa, Gwamna Usman Ododo, wanda ya taba raka shi zuwa ofishin EFCC a baya, ba ya cikin wadanda suka raka shi.