Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa (EFCC), ta tirela guda 21 makare da kayan abinci da za a fitar zuwa kasashen ketare.
EFCC ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta fitar ranar Talata da daddare a shafinta na Intanet.
- Bai Kamata Jama’a Su Tsorata Da Bullar Zazzabin Lassa A Adamawa Ba – Kwamishinan Lafiya
- Daga Bisani Dai Ta Tabbata Dubai Ta Ɗage Haramcin Biza Ga ‘Yan Nijeriya
Ta ce jami’anta sun kama tirelolin ne a kan hanyar Kalabiri/Gamboru Ngala da Bama da ke Jihar Borno.
“Ranar Talata, 5 ga watan Maris, 2024, jami’an EFCC shiyyar Maiduguri sun kama manyan motoci guda 21 makare da kayan abinci da kuma wadanda ba na abinci ba a kan hanyarsu ta zuwa birnin N’djamena na kasar Chadi, da Jamhuriyar Tsakiyar Afirka da Kamaru,” in ji sanarwar.
EFCC ta kara da cewa bincikenta ya gano cewa “an yi dabara ne aka boye kayan abincin a cikin manyan motocin ta yadda ba za a gane ba, amma ba mu yi kasa a gwiwa ba wajen gano ba.”
Ta ce an soma gudanar da bincike kan mutanen da aka kama a cikin manyan motocin kuma za a gurfanar da su a gaban kotu da zarar an kammala binciken.
“Ana sa rai kamen da aka yi wa motocin zai rage karancin abincin da ake fama da shi a fadin kasar nan sakamakon ayyukan fasa-kwauri.”
Gwamnatin Tarayya ta zargi masu fasa-kwauri na da hannu a tashin farashin kayan abinci a Nijeriya.
A watan da ya gabata, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce an kama manyan motoci guda 45 dauke da kayan abinci da za a fitar daga kasar nan.
Ya kara da cewa sun gano barauniyar hanya guda 32 da ake fitar da abinci daga Nijeriya.
Har yanzu dai ana ci gaba da fuskantar hauhawar farashin kayan abinci a Nijeriya.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp