Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya ƙaryata zargin cewa yana ƙarƙashin jagorancin siyasar tsohon gwamna, Malam Nasir El-Rufai, inda ya ce shugabannin da suka yi masa jagoranci tun farko sun haɗa da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma marigayi lauya mai kare hakkin dan Adam, Cif Gani Fawehinmi.
A cikin hirarsa da gidan talabijin na TVC, Gwamna Sani ya ce ba ya ganin dacewar ya tsaya yana musayar kalamai kan batun jagoranci, yana mai jaddada cewa burinsa shi ne samar da ingantaccen mulki ga al’ummar Kaduna.
- Hatsarin Jirgin Kasa: Gwamna Uba Sani Ya Ba Da Umarnin Talllafawa Fasinjojin Da Ke Cikin Jirgin
- An Cafke Mutum 22 Kan Kisan ‘Yan Ɗaurin Aure A Filato – Uba Sani
Ya kuma musanta raɗe-raɗin cewa gwamnatinsa tana biyan kuɗin fansa ga ’yan bindiga, yana mai bayyana hakan a matsayin ƙarya da wasu ’yan siyasa ke yaɗa wa don samun abin faɗa. “Ba mu taba biyan ko sisi ga wani ɗan bindiga ba. Waɗanda ke iƙirarin haka suna ƙoƙarin yaudaran jama’a ne kawai,” in ji shi.
Gwamnan ya bayyana cewa gwamnatin sa tana amfani da dabarun tsaro ta fuskar Soji da kuma ta hanyar tattaunawa tare da shugabannin al’umma domin shawo kan matsalolin tsaro, musamman a Birnin Gwari, inda ya ce tsarin haɗin kai na al’umma ya fara haifar da sakamako.
Kan rikicin da ya ɓarke a wani taron jam’iyyar adawa kwanan nan a Kaduna, Gwamna Sani ya nesanta kansa daga lamarin, yana mai cewa shi a matsayinsa na wanda aka taɓa tsarewa sau biyar saboda fafutukar kare doka da ’yanci, ba zai taba mara baya ga wani abu da zai take dimokuraɗiyya ba. Ya ce ya fi mayar da hankali kan ci gaban jama’a da kuma tabbatar da adalci a tafiyar da mulki.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp