Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya bayyana cewa ya gaji bashin dala miliyan 587, da Naira biliyan 85, da kuma kwanten ayyukan kwangila 115 daga gwamnatin Nasir El-Rufai.
Sai dai ya ce duk da dimbin bashin da ya gada, har yanzu bai ci bashin kobo daya ba a cikin watanni tara da hawa mulki.
- Hanyoyin Da Za A Taimaka Wa Malamai Inganta Aikinsu (5)
- Dambarwar Amal Umar Da ‘Yansanda, Ina Aka Kwana?
Gwamnan, ya bayyana hakan ne, a Kaduna ranar Asabar yayin da yake jawabi a wajen wani taro.
Ya ce dimbin bashin da ake bin jihar, ya sanya a yanzu gwamnatin ba ta iya biyan albashi.
Ya bayyana cewar a watan Maris gwamnatin jihar ta ware Naira biliyan bakwai wajen biyan bashi daga cikin Naira biliyan 10 da Gwamnatin Tarayya ta ware mata.
Gwamnan ya koka kan yadda El-Rufai ya bar wa jihar Naira biliyan uku a cikin asusunta, wanda ya gaza biyan albashin biliyan 5.2 da ake biyan ma’aikatan jihar.
Sai dai ya tabbatar da cewar bashin da ake bin jihar ba zai hana gwamnatinsa samar da ayyukan ci gaba a jihar ba.
A cewar gwamnan, “Duk da dimbin bashin Dala miliyan 587, da Naira biliyan 85, da kuma kwangiloli 115 da muka gada daga gwamnatin baya, amma mun jajirce wajen ganin jihar Kaduna ta samu ci gaba.”
Gwamna Sani ya bayyana wasu manyan abubuwan da gwamnatinsa ta sa gaba a shekarar 2024 da suka hada da samar da tsaro, samar da ababen more rayuwa, bunkasa ilimi, gina gidaje.
Da yake jawabi a wajen taron, tsohon babban hafsan sojin kasa, Janar Martin Luther Agwai (mai ritaya), ya bukaci gwamnatin jihar ta yi kokarin samar da magance matsalolin tsaro da jihar ke fuskanta.
A nasa jawabin, Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamali, ya yi wa gwamnatin fatan alheri, duk da kalubalen da jihar ke fuskanta.