Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai, ya hakura gami da cire ransa daga sha’awar zama minista a karkakashin mulkin shugaba Tinubu kamar yadda jaridar Premium Times ta nakalto.
Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta ce, Nasir El-Rufai ya shaida wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu yayin wata ganawa da suka yi a ranar Talata cewa, shi kam yanzu bai da ra’ayin zama minista, amma duk da hakan zai bada tasa gudunmawar wajen cigaban Nijeriya a matsayinsa na dan kasa.
- Mun Dauki Darasi A Zaben 2023 – Shugaban INEC
- Sin Ta Kara Ware Yuan Biliyan 1.46 Don Taimakawa Wadanda Ambaliyar Ruwa Ta Shafa
“Ya shaida wa shugaban kasa cewa ya na son ya maida hankalinsa kan darasin dakta a jami’ar The Netherlands,” a cewar daya daga cikin majiyoyin.
Wata majiyar kuma ta shaida cewar tsohon gwamnan ya bada shawarar a zabi Jafaru Ibrahim Sani daga jihar Kaduna a matsayin minista da zai maye gurbin ta’ayin da aka masa da farko, a cewarsa, shugaban kasa zai samesa a matsayin mutum mai matukar amfani.
Shi dai Sani ya yi aiki a matsayin kwamishina a ma’aikatu har uku a karkashin mulkin gwamna Nasiru El-Rufai.
Nasiru dai ya gana da shugaban kasa a fadar shugaban kasa da ke Abuja bayan da majalisar dattawa ta tantance da amincewa da zabin ministoci 45 cikin 48 da shugaban kasa ya aike musu.
Kodayake, majalisar ta ki amince da zabin Nasir El-Rufai da wasu mutum biyu bisa rahoton tsaro da bai amince da su ba.
Sauran mutum biyun da majalisar ta ki amince da nadinsu su ne tsohon sanata daga Taraba, Sani Danladi, da kuma Stella Okotete daga jihar Delta.
Majiyoyin sun ce a lokacin da El-Rufai ya ji matakin da Majalisa ta tsayar kansa yana ma can kasar Landan nan da nan ya dawo Nijeriya a ranar Litinin domin neman ganawa da shugaban kasa kan batun.
A cewar majaliyar a yayin zaman shugaban kasa da El-Rufai, Tinubu ya fada masa cewar ya amshi wasu korafe-korafe a kan nadin da ya amsa na minista.
Sai dai shugaban ya nemi awanni 24 domin ya sake bibiyar korafe-korafen da rahoton tsaro na SSS domin ganin an samu damar da majalisa za ta iya amincewa da shi.
A lokacin ne sai El-Rufai ya amsa da cewa shi yanzu ba ya da ra’ayin zama minista kuma, tun da wasu da suke makale a jikin shugaban kasan ba su da ra’ayin zamansa minista.
Lokacin da aka tuntubi kakakin Malam Nasir, Muyiwa Adekeye, ya ki cewa uffan kan labarin.