Jam’iyyar APC mai mulki ta ce tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, na fushi ne saboda bai samu kujerar minista ba a gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
A wata sanarwa da ta fitar, jam’iyyar ta ce kalaman da El-Rufai ya yi a wata hira da BBC Hausa na nuna cewa yana ƙorafi ne kan rashin ba shi mukamin minista, wanda hakan ne ya sa shi barin jam’iyyar zuwa SDP.
- Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [11]
- Kokarin Kasar Sin Na Bunkasa Hadin Gwiwar Neman Ci Gaban Duniya Na Nan Daram
“El-Rufai bai ji daɗin yadda Shugaba Tinubu da gwamnatinsa suka yi masa ba kan batun rashin ba shi kujera, shi ya sa yake sukar jam’iyyar da ta kai shi ga nasara a siyasa,” in ji APC.
Jam’iyyar ta ƙara da cewa ‘yan Nijeriya sun fi yadda El-Rufai ke musu kallon basira, kuma sun fahimci cewa yana yi ne don kansa, ba don damuwa da ƙasar ba.
APC ta ce ba ta damu da kalaman El-Rufai ba, domin tana samun sabbin mambobi masu tarin yawa da ke mara wa Shugaba Tinubu baya.
Daga ƙarshe, jam’iyyar ta ce kiran da El-Rufai ke yi ga ‘yan adawa da su shiga SDP ba komai ba ne illa ƙoƙarin biyan buƙatun kansa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp