Mamallakin kafar sada zumunta ta Twitter, Elon Musk, ya zarce tsohon shugaban kasar Amurka, Barack Obama, a matsayin wanda ya fi yawan mabiya.
Binciken da wakilinmu ya yi a Twitter, ya nuna cewa a yanzu Elon Musk na da mabiya miliyan 133.1, yayin Barrak Obama ke da miliyan 133.
- Saura Wasanni 10 Arsenal Ta Lashe Kofin Firimiyar Ingila
- Tsohon Mataimakin Sakataren NUJ Zai Kai INEC Kotu Kan Zaben Gwamnan Jihar Kaduna
Tun lokacin da ya mallaki Twitter kan kudi dala biliyan 44 a ranar 14 ga watan Afrilu, 2022, mabiya Musk suka karu daga miliyan 35 zuwa miliyan 133.1.
A cikin watan Yuni 2022, ya zama mai amfani mutum shida a kafar da ya fi kowa yawan mabiya.
Duk da yawaitar yawan mabiya, attajirin da ya fi kowa arziki a duniya yana bin mutane 186 kawai a kafar.