Tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya yi watsi da rahoton binciken da ya bayyana cewar ya bude asusun bankuna har guda 593, wadanda yayi amfani da su wajen boye makudaden kudaden gwamnati a ciki.
Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, Emefiele, wanda aka bayar da belinsa a ranar Juma’a, ya ce tuni ya bai wa lauyoyinsa umarnin shigar da kara kan rahoton da ya ce babu abin da ya kunsa sai karairayi domin bata masa suna.
- ‘Yan Ta’adda Sun Kashe Mutane 2 A Ranar Kirsimeti A Adamawa
- Gwamnatin Sakkwato da Wamakko Sun Tallafa Wa Mutane 66 Da Sojoji Suka Ceto
Cikin rahoton binciken da ya shafe sama da watanni hudu yanayi, Jim Obazee da shugaba Bola Tinubu ya dora wa nauyin aikin, ya bayyana cewar tsohon gwamnan na CBN ya bude daruruwan asusun bankunan da ya gano.
Ya ce asusun ba tare da izinin hukumar gudanarwar babban bankin aka bude su ba, ko kuma na tsohon shugaban kasa (Muhammadu Buhari) ba.
Kazalika, rahoton ya kuma bayyana gano fam dubu 543 da 482 da Emefielen ya boye a asusun wasu bankuna da ke Birtaniya.
Wani batu da binciken kwamitin na musamman din ya gano kuma shi ne yadda ake tuhumar Godwin Emefiele da bin wasu haramtattun hanyoyi wajen saye bankunan Union, da Keystone da kuma Polaris.