A satin da ya gabata ne hukumar kwallon kafar Nijeriya, NFF ta tabbatar da daukar Éric Sékou Chelle a matsayin sabon kocin kungiyar kwallan kafa ta Super Eagles kuma kamar yadda sanarwar ta tabbatar nadin Chelle ya fara aiki ne nan take inda a cewar hukumar NFF ta yanke shawarar daukar sabon kocin ne daga ketare a zaman da ta yi ranar 2 ga watan Janairun wannan shekarar ta 2025.
NFF ta ce babban aikin da ta dora wa tsohon kocin dan asalin kasar Mali shi ne: kai Nijeriya Gasar Kofin Duniya ta 2026, abin da masana kwallon kafa a nahiyar Afirka da ma Nigeriya suke ganin da kamar wuya ganin yadda rukunin da Nigeriya take ciki yake da kuma kalubalen da ke gaban samun tikitin zuwa gasar ta cin kofin duniya da zai fara jagorantar Nigeriya a cikin wannan shekarar.
- Kar Ku Tayar Da Hankalinku Kan Cutar Tsuntsaye – Ma’aikatar Lafiya Ta Kano
- Duniya Na Fatan Sin Da Amurka Za Su Cika Alkawuransu Cikin Hadin Gwiwa
Waye Éric Sékou Chelle
Ba kamar sauran fitattu a harkar kwallon kafar Afirka, irin su George Weah da Abedi Pele da Samuel Eto’o da Rashidi Yekini da sauransu ba, Eric Chelle ba fitacce ba ne a kwallon kafar Afirka, dalili kuwa shi ne a lokacin da yake dan wasa bai wani shahara sosai ba saboda a lokacin da yake buga wasa, sau biyar kawai ya buga wa babbar tagawar kwallon kwallon kafar kasarsa, Mali wasa. Dangane da matakin kungiyoyi kuwa, ya buga wasa ne yawanci a kananan kungiyoyin Faransa, irin su Martigues da Balenciennes da Lens da Istres da kuma Chamois Niortais. To sai dai Chelle ya bai wa mutane da dama mamaki a matakin koci saboda irin kokarin da ake ganin ya yi domin kafin ya zama kocin babbar tawagar Mali, ya rike wasu kungiyoyin Faransa da ke buga karamar gasar kasar.
Chelle, mai shekara 47 ya samu kwarewa a aikin horarwa ne a kungiyoyin GS Consolat, FC Martigues, MC Oran and Boulogne kuma a shekarar 2022 ce Mali ta nada shi a matsayin wanda zai jagoranci babbar tawagar kasar, kuma ya bayar da mamaki bayan ya kai kasar gasar cin Kofin Afirka ta 2023 da aka gudanar a Ibory Coast inda a gasar ce, Mali ta samu nasarar kai wa matakin kwata-fainal, kafin mai masaukin baki ta fitar da ita a karin lokaci, sai dai bayan gasar ne kasar ta kore shi a watan Yunin 2024.
‘Rike Super Eagle ba karamin aiki ba ne’
Amma kuma aikin horar da Nijeriya babban aiki ne da ke bukatar kwarewa da jajircewar koci, la’akari da yadda kasar nan ke da fitattun ‘yan wasa da ke buga wasa a wasu manyan kungiyoyin Turai wanda hakan yake nufin ko a wajen gayyatar ‘yan wasa akwai babban aiki a wajen mai koyar da tawagar Nigeriya saboda akwai ‘yan wasa da yawa kuma suna kokarin da ya kamata a gayyace su.
To amma duk da kwararrun ‘yan wasa da kasar nan ke da su, tana fama da matsalar samun nasarorin da ake bukata a wasanninta, musamman a Afirka kuma mutane da alama na alakanta rashin katabus da Super Eagle ke yi da rashin kwararren koci, wanda zai iya hada fitattun ‘yanwasan da kasar ke da su domin hada tawaga mai karfin da za ta lashe babbar gasa.
Masu koyarwa da dama – na ciki da wajen kasar nan sun zo, sun kuma tafi, amma babbar tambayar da ke yawo a bakunan ‘yan Nigeriya, shi ne shin
Eric Chelle zai iya fitar wa Super Eagles kitse daga wuta?
Cikin sanarwar nadin nasa, NFF ta dora masa alhakin kai Nijeriya gasar Kofin Duniya domin a yanzu haka kasar nan na matsayi na biyar a kan teburin neman gurbin shiga gasar Kofin Duniya ta 2026 da maki uku, bayan da ta ji jiki a hannun Benin da Lesotho sannan wasannin farko da Chelle zai fuskanta a neman gurbin Gasar Kofin Duniya ta 2026 su ne a watan Maris inda zai buga wasanni biyu. Amma kuma a yanzu hankula sun koma kan sabon kocin domin ganin irin rawar da zai taka wajen farfado da Super Eagles.