Dan wasan kasar Denmark, Christian Eriksen, ya amince da komawa kungiyar kwallon kafa ta Manchester United.
Dan wasan, wanda ya buga wasanni na watanni biyar a kungiyar Brentford, ya sanar da kocin Manchester United ne da safiyar yau.
- HOTUNA: Yunkurin Tsige Kakakin Majalisar Dokokin Bauchi, ‘Yan Sanda Sun Rufe Majalisar
- Kalvin Phillips Ya Koma Manchester City Daga Leeds United
Tsohon dan wasan Tottenham din, ya kamu da cutar bugun zuciya a yayin da ake buga wasanni cin kofin Nahiyar Turai na 2020 da Italiya ta lashe.
Kawo yanzu dai dan wasan zai saka hannu a kan yarjejeniyar shekara uku da zarar an kammala duba lafiyarsa a Manchester United.
Shi ne dan wasa na biyu da ake saran Manchester United za ta saya bayan cimma matsaya da Tyrrell Malacia daga Feyernood.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp