Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana Etsu Nupe, Mai Martaba Alhaji Yahaya Abubakar, a matsayin ginshiƙi na zaman lafiya da haɗin kai a Nijeriya, wanda ya sadaukar da rayuwar sa wajen bunƙasa masarautar Nupe, Jihar Neja, da ƙasa gaba ɗaya.
A cikin saƙon taya murna na zagayowar ranar haihuwar sa ta 73 da kuma cika shekara 22 a kan karagar mulki, Ministan, wanda shi ne Kakakin Nupe, ya ce: “Etsu Nupe mutum ne mai jajircewa wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai, wanda a cikin shekaru 22 da suka gabata ya jagoranci ƙasar Nupe zuwa cigaba da bunƙasar da ba a taɓa ganin irin ta ba.”
Idris ya jaddada rawar da Sarkin Mai Daraja ta Ɗaya ya taka wajen ƙarfafa haɗin kan Nijeriya, tun daga gudunmawar sa a rundunar sojin ƙasa har ya kai matsayin Birgediya Janar, zuwa irin gudunmawar da yake bayarwa a matsayin Shugaban Kwamitin Tsara Ayyuka na Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Nijeriya.
Ya ƙara da cewa: “Don haka taya ɗaya daga cikin shugabannin Nijeriya mafiya sauƙin kai, masu karamci da jarumtaka, murnar zagayowar ranar haihuwar sa, da roƙon Allah ya ci gaba da yi masa jagora a babban nauyin shugabanci na ƙasar Nupe da jama’ar ta, ya kuma ƙara masa ƙarfi don ci gaba da aiki wajen tabbatar da zaman lafiya, haɗin kai, da cigaban Nijeriya.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp