Kungiyar Tarayyar Turai (EU) ta ware Euro miliyan daya (€1m) don samar da agajin gaggawa ga ‘yan Nijeriya da ke fama da matsalar ambaliyar ruwa da kuma yaki da yaduwar cutar kwalara.
Wannan tallafi zai taimaka wajen kula da mutanen da ambaliyar ruwa da cutar kwalara suka shafa, wanda hakan ya kawo jimillar kudin da EU ta kashe a Nijeriya cikin wannan shekara zuwa Euro miliyan arba’in da takwas da digo bakwai (€48.7m).
- Kasar Sin Ta Yi Kira Da A Hada Karfi Da Karfe Wajen Samar Da Yanayin Da Zai Dace Da Warware Matsalar Sudan
- CBN Zai Ci Tarar Bankuna Naira Miliyan 150 Da Aka Kama Suna Sayar Da Sabbin Takardun Naira
Sama da rabin wadannan kudade an kashe su ne a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma saboda tsananin karancin abinci da matsalar yara masu fama da cutar tamowa sakamakon rashin tsaro a yankunan.
A cewar sanarwar da ofishin jakadancin EU a Nijeriya ya fitar, wannan kudi zai kasance a rukuni biyu: Euro dubu dari biyar (€500,000) domin tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa, sannan Euro dubu dari biyar (€500,000) domin shawo kan matsalar kwalara.
Kudaden za su taimaka wa kungiyoyin agaji wajen samar da mafaka, tsaftataccen ruwan sha, tsaftar muhalli, da kula da lafiya a yankunan da ake fama da wadannan matsaloli.
Tallafi Ga Jihohin Da Ambaliyar Ruwa Ta Fi Shafa
Domin tallafawa jihohin da ambaliyar ruwa ta fi shafa, kungiyar EU ta ware Euro dubu dari biyar (€500,000) musamman ga jihohin Kogi, Delta, da Anambra.
Wadannan jihohi sun kasance daga cikin wuraren da ambaliyar ta fi muni, kuma ana hasashen yiwuwar sake samun wata ambaliyar ruwa.
Ambaliyar da ta faru ta shafi mutane sama da dubu saba’in da takwas (78,000), tare da lalata dubban gidaje da gonaki, musamman a garuruwan da ke kusa da kogunan Neja da Benue.
Wannan kudi zai taimaka wajen samar da mafaka, tsaftataccen ruwa, da kare lafiyar mutanen da abin ya shafa, tare da tabbatar da cewa akwai shirin gaggawa idan aka sake samun sabuwar ambaliya.
Tallafi Don Shawo Kan Matsalar Kwalara
Baya ga tallafin ambaliyar ruwa, kungiyar EU ta ware Euro dubu dari biyar (€500,000) domin yaki da cutar kwalara.
Wannan cuta ta haddasa matsaloli da dama, musamman a garuruwan da ambaliyar ruwa ta shafa, inda rashin tsaftar muhalli da tsaftataccen ruwan sha ke kara ta’azzara yaduwar cutar.
Jihohin Borno da Yobe sun kasance daga cikin yankunan da cutar kwalara ta fi shafa, sakamakon karancin matsuguni a sansanonin ‘yan gudun hijira da rashin tsaftataccen ruwan sha.
Wannan tallafi zai taimaka wajen inganta fannin lafiya ta hanyar samar da cibiyoyin kula da marasa lafiya, tsaftace muhalli, riga-kafin kwalara, da kuma samar da tsaftataccen ruwa.
Taimakon Da Aka Gabatar a Watan Satumba
A watan Satumba na wannan shekara, EU ta kara samar da Euro miliyan daya da digo daya (€1.1m) domin tallafawa masu aikin agaji a Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.
Wannan tallafi ya kasance wani bangare na shirin EU na tallafawa kasashen yammacin da tsakiyar Afrika wajen shawo kan matsalolin ambaliyar ruwa da sauran iftila’i.
Tallafin EU zai taimaka wajen magance kalubalen da Nijeriya ke fuskanta sakamakon ambaliyar ruwa da cutar kwalara, tare da tabbatar da cewa mutanen da abin ya shafa sun samu kulawa.