Ƙungiyoyi da ƙasashen duniya sun yi jimami da ta’aziyyar rasuwar tsohon Shugaban Nijeriya, Muhammadu Buhari, wanda ya rasu a wani asibiti da ke birnin Landan a ranar Lahadi, kuma aka binne shi a ranar Talata a garinsu Daura, Jihar Katsina.
Ofishin Tarayyar Turai (EU) a Nujeriya ya wallafa saƙon ta’aziyyarsa a kafar sada zumunta.
- Sin Ta Yi Nasarar Harba Kumbon Dakon Kaya Na Tianzhou-9
- Yawan Karuwar GDPn Sin A Rabin Farkon Bana Ya Kai 5.3%
EU ta yaba wa Buhari bisa shekara takwas da ya yi yana shugabancin Nijeriya, inda ta ce yana da kishin haɗin gwiwar ƙasa da ƙasa da bin doka a harkokin duniya.
“EU na miƙa ta’aziyyarta ta musamman ga al’ummar Nijeriya bisa rasuwar tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. A lokacin mulkinsa, Buhari ya nuna goyon baya ga haɗin gwiwa da kuma tsarin dokokin duniya,” in ji sanarwar.
Haka kuma, ofishin jakadancin Turkiyya a Abuja ya miƙa saƙon ta’aziyyarsa ga Nijeriya.
Jakadan Turkiyya a Nijeriya, Mehmet Poroy, ya yi masa addu’a domin samun rahamar Allah.
Tun da farko, Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya fitar da sanarwa a shafinsa X, inda ya miƙa ta’aziyya ga ’yan Nijeriya bisa rasuwar tsohon shugaban.
Sanarwar ta ce rayuwar Buhari cike ta ke da hidima, ladabi da jajircewa wajen gaskiya a shugabanci.
Gwamnatin ƙasar China ma ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ta hannun ofishin jakadancinta da ke Abuja a shafin X a ranar Lahadi.
Sun yaba wa Buhari tare da nuna baƙin ciki game da rasuwarsa.
Sanarwar ta ce: “Ofishin jakadancin ƙasar China a Nijeriya na miƙa ta’aziyyarsa ta musamman ga al’ummar Nijeriya bisa rasuwar tsohon Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp