Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton ta sanar da sallamar kocinta, Sean Dyche daga muƙaminsa saboda rashin samun sakamako mai kyau a ƙarƙashin jagorancinsa.
Dyche, wanda ya shafe ƙasa da shekaru biyu yana jagorantar ƙungiyar, ya samu takardar sallama bayan ƙungiyarsa ta ci gaba da taɓarɓarewa.
- Sin Ta Ciri Tuta A Fannin Ingiza Koyi Da Juna Tsakanin Mabanbantan Wayewar Kai
- Jami’an Tsaro Sun Kawar Da Ƙasurgumin Ɗan Bindiga Baƙo-baƙo Da Mayaƙansa A Katsina
Sanarwar korarsa ta fito ne sa’o’i kaɗan kafin Everton ta karɓi baƙuncin Peterborough United daga gasar League One a zagaye na uku na gasar cin kofin FA.
Ƙungiyar ta ce Leighton Baines, kocin ‘yan ƙasa da shekaru 18, da kyaftin ɗin ƙungiyar, Seamus Coleman, za su jagoranci Everton a wannan wasan.
Bayan korar Dyche, wasu daga cikin ma’aikatan horar da ƙungiyar, ciki har da Stone, Mark Howard, da Billy Mercer, suma sun bar ƙungiyar.
A yanzu haka, Everton na matsayi na 16 a teburin gasar Firimiyar Ingila, bayan da Bournemouth ta doke ta da ci 1-0 a satin da ya gabata.
Wannan kakar ta zama ta ƙarshe ga Everton a filin Goodison Park mai shekaru 132 kafin ta koma sabon filinta da ke Bramley-Moore Dock a birnin Liverpool.