• English
  • Business News
Sunday, November 9, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fada Ya Barke Tsakanin Shugabannin ’Yan Bindiga, 2 Sun Mutu Yayin Rikicin A Zamfara

by Muhammad
3 years ago
Fada

Fadan ‘yan bindigar ya kai ga kashe wasu manyan shugababbin bangarorin biyu da suka hada da Dulhu da kuma Dan Maigari, tare da yaransu sama da 15 a rikici da ya barke tsakaninsu a dajin Zamfara.

Aminiya ta rawaito wani kazamin fadan ya kaure ne a safiyar Talata tsakanin bangaren kasurgumin dan bindiga, Bello Turji da wancan bangaren na ’yan bindigar da suka dade ba sa ga-maciji da juna.

  • ‘Yan Bindiga Sun Sako Wasu Mutum 2 Da Suka Sace A Wata Cocin Jihar Abiya 
  • Kisan ‘Yan Arewa A Kudu: An Bukaci Gwamnati Ta Gaggauta Daukar Mataki

Wani ganau ya shaida wa Aminiya cewa, “Turji ya yi garkuwa da wadansu mutane, amma mun ji an ce daga baya ya kashe su; an bar gawar Dulhu na da sauran yaransa a maboyarsa.

“Shi kanshi Turji ana kyautata zaton an kashe yaransa a musayar wutar, amma ba a san ko mutum nawa ba ne; amma na ga wadansu daga cikinsu ana komawa da su, dauke da raunin harbi.”

Bangaren Turji da su Dulhu sun yi musayar wutar ne kan zargin kashe wani dan bindiga da ke karkashin wani yaron Bello Turji, wanda ake kira Na-Sanda.

LABARAI MASU NASABA

Matashi Ya Kashe Ɗan Acaɓa Don Neman Kuɗin Auren Mace Ta Uku A Bauchi

Matashi Ya Kashe Kakanninsa Kan Abinci A Kano

Aminiya ta gano a kan haka ne Turji ya jagoranci yaransa suka kai harin ba-zata a maboyar su Dulhu da ke Maniya, inda suka kashe ’yan bindiga da dama.

Daga cikin ’yan bindigar da su Turji suka kashe har da Dulhu da Dan Maigari, wanda kani ne ga Bashari Maniya, tsohon dan bindiga da yanzu ya zama mai shiga tsakani domin sasantawa tsakanin ’yan bindiga da gwamnati.

Ganau a kauyen Dangondi sun shaida wa Aminiya cewa sun ga ’yan bindiga da dama daga Maniya suna tsallaka babban titin Moriki zuwa Shinkafi, domin tserewa da rayuwarsu, ta cikin dajin Sabubu.

Wakilin Aminiya a Gusau ya nemi samu karin bayani daga kakakin ’yan sandan Jihar Zamfara, SP Shehu Muhammad, amma bai amsa kiran waya ko rubutaccen sakon da wakilin namu ya yi mishi ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Al'ajabi

Matashi Ya Kashe Ɗan Acaɓa Don Neman Kuɗin Auren Mace Ta Uku A Bauchi

October 17, 2025
Yadda Waliyin Amarya Ya Sace Sadaki A Kano
Al'ajabi

Matashi Ya Kashe Kakanninsa Kan Abinci A Kano

September 25, 2025
Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye
Al'ajabi

Al’ajabi: Yadda Aka Shirya Bikin Haihuwar ‘Ya’yan Awaki Biyar A Garin Dakasoye

September 17, 2025
Next Post
Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Shugabancin Jam’iyyar APC Ta Kasa

Sabon Rikici Ya Kunno Kai A Shugabancin Jam'iyyar APC Ta Kasa

LABARAI MASU NASABA

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

An Rufe Taron Kolin Wuzhen Na Ayyukan Yanar Gizo Na Duniya Na Shekarar 2025

November 9, 2025
Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

Katsina United Ta Shiga Komar Hukuncin Hukumar NPFL

November 9, 2025
Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

Xi Ya Gana Da Shugabar IOC Tare Da Shugaban IOC Na Karramawa

November 9, 2025
CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

CMG Ya Cimma Yarjejeniyar Samun Iznin Watsa Shirye-shiryen Wasannin Olympics Daga Shekarar 2026 Zuwa 2032

November 9, 2025
Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

Kasar Sin Ta Yi Nasarar Harba Sabbin Taurarin Dan Adam Na Gwaji

November 9, 2025
Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

Shugaba Xi Ya Ayyana Bude Gasar Wasanni Ta Kasa Karo Na 15

November 9, 2025
Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

Mizanin Farashin Kayan Masarufi Na Kasar Sin Ya Karu Da 0.2% A Watan Oktoba

November 9, 2025
Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

Me Ke Haddasa Yawaitar Farmakar Ƴan Wasa A Gasar Firimiyar Nijeriya

November 9, 2025
NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

NBA Ta Yi Allah Wadai Da Yadda Hukuncin Alƙalai Ke Karo Da Juna

November 9, 2025
Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

Mataimakin Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kebbi Bagudo Ya Shaƙi Iskar ‘Yanci Daga ‘Yan Bindiga

November 9, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.