Fadar Shugaban Ƙasa, ta ce ba gaskiya ba ne cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba shi da lafiya kuma ana shirin kai shi ƙasar waje domin nema masa magani.
A makon da ya gabata, cibiyar binciken labarai ta ICIR ta ce ta samu labari daga wata majiyarta cewa tawagar likitocin shugaban ƙasa na shirin fitar da shi waje domin jinya.
- Babban Dalilin EFCC Na Yi Wa Tsohon Gwamnan Sokoto, Tambuwal, Tambayoyi
- Tireloli Sun Yi Taho Mu Gama, Mutane 4 Sun Jikkata A Titin Zariya–Kaduna
ICIR ta rubuta a shafinta cewa rahotanni na nuna shugaba Tinubu yana kwance ba ya iya fita.
Hakan ya sa ba ya gudanar da wasu ayyukan mulki.
A cewar rahoton, Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya wakilce shi a wasu ayyukan gwamnati.
Sai dai wasu daga cikin hadiman shugaban kamar Abdulaziz Abdulaziz, mai taimaka masa a kafafen watsa labaru, ya ce labarin ba gaskiya ba ne.
Batun rashin lafiyar Tinubu ba sabon abu ne, domin tun yana yaƙin neman zaɓen takara a 2023 ake kai ruwa rana kan batun.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp