• English
  • Business News
Monday, May 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fahimtar Hakikanin kasar Sin

by Rabi'u Ali Indabawa and Sulaiman
4 hours ago
in Labarai
0
Fahimtar Hakikanin kasar Sin
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Sunday Isuwa wanda kwanan nan ya dawo daga kasar Sin bayan shafe makwanni biyu domin halartar taron kara wa juna sani kan shugabannin ‘yan jarida da Cibiyar Kula da Harkokin Kasuwanci ta kasa da kasa (AIBO) ta shirya a ma’aikatar kasuwanci ta Jamhuriyar Jama’ar Sin a birnin Beijing, ya yi rubutu kan hakikanin kasar Sin.

A Nijeriya da galibin kasashen Afirka, idan mutum ya ambaci kasar Sin, ya kan nuna hotunan kayayyakin da ba su da inganci. Yana tuna wa mutanen da suke kama da junansu kuma ma su gajarta, sannan yana jawo tunanin mutane masu kwazo da suke kokarin su ci gaba da biyan bukatun kansu.

  • ‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3, Sun Sace 26 A Zamfara
  • Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Bisa Daidaito A Afirilu

Ko da yake, bayan da jirgin saman da na shiga ya shafe kimanin sa’o’i 16 yana tafiya daga Abuja, Nijeriya, tunanina ya canja sosai, bayan saukarsa a Birin Beijing, Babban Birnin Jamhuriyar Jama’ar Sin (PRC).

Kalmar da Mutane ke amfani da ita kan al’ummar Sin na da nauyi. kalubalen na nuni da ra’ayin cewa mutanen kasar Sin kabila ce guda daya, gajeru, masu samar da kaya marasa inganci.

Na kalli wannan katafaren gini na kuma taka matakalarsa, na fara tunanin irin jajircewar mutanen kasar Sin wadanda suka gina katangar da ta taso daga kasarsu ta haihuwa zuwa Mongoliya.

Labarai Masu Nasaba

Gwamna Nasir Ya Naɗa Sabbin Sakatarori Na Ƙananan Hukumomi 21 A Kebbi

Kotu Ta Daure Wasu Mutane 3 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Mutum A Gidan Yarin Adamawa

Hawa wannan babbar katangar na koyar darussa masu masu ma’ana,- daya daga cikinsu shi ne tsayin daka da ya kai ga Sinawa zuwa ga samun daukaka. Wannan gogewa ta nuna kyakkyawar dabi’ar aikin Sinawa, wanda ya ba da gudummawa ga ci gaban da suka samu a cikin shekaru 40 da suka gabata.

Kafin wannan lokacin, jami’ar Yang Boazhin ya lura cewa, kasar Sin ta fi sauran sassan Afirka talauci. Ta ba da labarin ziyarar da ta kai Afirka a shekarar 1985 a matsayin jami’ar diflomasiyya, inda ta tabbatar da cewa Afirka na da gagarumin ci gaba a wannan lokacin.

Jamhuriyar kasar Sin, mai yawan al’umma biliyan 1.4, ta kunshi gundumomi hudu da larduna 23, tare da yankuna biyar masu cin gashin kansu da ke wakiltar kabilu daban-daban, da yankuna 21 na musamman na gudanarwa.

Boazhin, jami’ar diflomasiyyar kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin na mutunta ‘yan tsiraru, shi ya sa ba a yi yakin basasa ba. Ta yi nuni da cewa, Hong Kong, a da tana karkashin mulkin Birtaniya, yanzu ta zama yanki na kasuwanci kyauta.

Ta kara da cewa, “Ana kwatanta kasar Sin da Turai domin tana da yawan al’umma wanda ya kai kashi uku bisa uku na Afirka. Muna da iyaka da kasashe makwabta 14, fiye da kowace kasa.

Boazhin ta bayyana cewa, Sarki kin Shi Huang ya hade kasar Sin a shekara ta 221 kafin haihuwar Isa Yesu Almasihu, ko da yake kasar ba ta bin tsarin tarayya. Gwamnatin ta yi juriyar zama na tsawon shekaru 2,000 a karkashin mulkin sarakuna 408 a cikin dauloli 16.

Katafariyar ganuwar ta kasar Sin, wacce a yanzu ta zama wani muhimmin wurin yawon bude ido, an gina ta ne da farko domin samar da tsaro, ba don fadadawa ba. Ta ratsa yankuna 15 kuma ta yi kokarin maido da guda 14 maidowa.

An fara habaka masana’antu na kasar Sin da kirkirar abin fashewa, da wata na’urar kwamfuta mai nuna alkibla, madabba’a, da kuma yin takardu- gudummawar da ta habaka wayewar dan’Adam.

Daular Song, daga karni na 10 zuwa na 13, ta fara bug takardu, yayin da Zheng He, fitaccen shugaba, ya fara binciken teku daga shekarar 1405 zuwa 1433.

Boazhin ta ce, “Ba mu taba bautar da mutane a Afirka ba, ko kuma ba mu kwace kasa ko tilasta wa wani ya koyi harshenmu tun kafin shekarar 1492, kuma muna da iko,” in ji Boazhin, inda ta bayyana tushen dabarun kasar Sin na ketare da ke da muhimmanci a yau.

Duk da karfin arzikin da take da shi a wancan lokacin, kasar Burtaniya ta mamaye kasar Sin a lokacin juyin juya halin masana’antu.

“Yakin Opium, wanda ya fara a shekara ta 1850, ya samo asali ne sakamakon shawarar da kasar Sin ta dauka na kona opium tare da haramta amfani da ita a tsakanin ‘yan kasarmu, wanda ya kai ga mamayewa daga kasashen yammacin Turai. A sakamakon haka, Shanghai ta mamaye, kuma Hong Kong ta fada karkashin ikon Birtaniya, wanda ya raunana al’ummarmu.”

A shekara ta 1911, Yat-sen ya jagoranci wani gagarumin juyin-juya hali wanda ya haifar da jamhuriyya, amma abin ya ci tura, wanda hakan ya ba da damar kafa jam’iyyar kwaminisanci ta kasar Sin a wannan shekarar, wanda daga karshe ya kai ga jagorancin da kasar Sin ke da shi a halin yanzu.

Mao Zedong ya kafa jamhuriyar jama’ar kasar Sin a shekarar 1949, mai jama’ar da yawanta ya kai miliyan 540. A yau, tsarin siyasar kasar Sin ya zama na gurguzu karkashin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin (CPC). Jam’iyyar CPC ta shafe shekaru 78 tana mulkin kasar, duk da cewa akwai wasu jam’iyyun siyasa guda takwas da ke ba da ra’ayi sabanin ra’ayi da ya dace da muradun kasa.

A shekarar 1953, kasar Sin ta gina cibiyar masana’antu ta farko ta kasa, tare da raya aikin gona don tabbatar da samar da abinci ga al’ummarta, har ma ta mayar da kashi 15 cikin 100 na yankunan hamada da tsaunuka zuwa gonaki.

A shekarar 1964, kasar Sin ta yi nasarar gwada bam din atomic da hydrogen.

A shekarar 1970, Deng diaoping ya ba da shawarar yin gyare-gyare don daukaka jama’a ta hanyar sauya tsarin gine-gine.

Shekarar 1978 ta kasance wani muhimmin lokaci ga jama’ar kasar Sin, wanda ya haifar da juyin juya halin al’adu, lokacin da kudin shigar kowane dan kasar Sin ya kai Dalar Amurka 156 kacal.

kasar Sin ta yi tsari na sauye-sauyen yankunan karkara, inda ta bai wa manoma damar ci gaba da kasancewa a cikin al’ummominsu, wasu daga cikinsu an yi musu lakabi da Hero Bay billage. An biya wa manoma diyya na zamansu, an ba su fili, an kuma ba da tallafi daban-daban.

A wannan lokaci, gwamnati ta kara farashin sayen hatsi, ta yadda za a rage yunwa. Sinawa suna alfahari da saukaka musu talauci.

Mallakar motoci masu zaman kansu ba abin damuwa ba ne ga mutane da yawa, saboda gyare-gyare a fannin sufuri ya hada dukkanin al’ummomi, kauyuka, da garuruwa ta hanyoyi daban-daban na jirgin kasa, motocin bas, hanyar intanet, samar da wutar lantarki, da wadata gari da haske.

Wadannan ci gaban da aka samu sun bude tattalin arzikin kasar Sin ga duniya, tun daga yankunan gabar tekun Hong Kong, wadanda suka jawo jarin kasar waje.

An kafa yankuna hudu na musamman na tattalin arziki, ciki har da Shenzhen, wani karamin kauye kusa da Hong Kong, yanzu cibiyar masana’antu. Shenzhen tana da yawan jama’a miliyan 18 da ma’aunin kudi na jimillar lasuwancin da aka samar wato (GDP) na Dala tiriliyan 3.68, wanda ya sanya ta a matsayin birni na 11 mafi girma a duniya.

Kasar Sin ta kafa tsarin tattalin arzikinta na gurguzu a shekarar 1992, sannan ta shiga kungiyar WTO a shekarar 2001, tare da saukaka kasancewar kayayyakin kasar Sin a duniya.

Shekaru 40 na yin gyare-gyaren da aka yi a baya sun inganta tattalin arzikin kasar Sin sosai, tare da samun jari daga kamfanoni 450 na duniya.

bangaren kera motoci na kasar Sin ya samu bunkasuwa mai saurin gaske, yana sa kaimi ga mazauna birane.

kasar Sin ita ce babbar kasa a fannin fasaha, bayan da ta aiwatar da tsarin GPS a shekarar 2021.

A shekarar 2024, an samar da robobin masana’antu sama da 500,000 a kasar Sin, yayin da majalisar wakilan kasar Sin ta kafa manyan manufofi.

Jama’ar kasar Sin yanzu suna more tsawon rai saboda ingantaccen tsarin kiwon lafiya. Gwamnati tana ba da kulawa ta musamman ga yara, karancin mace-mace, da ayyukan sadaukarwa ga manyan ‘yan kasa, wadanda ba sa biyan kudin ayyukan jin dadi, gami da tallafin abinci.

Ilimi dole ne ga yara har zuwa shekaru tara, kuma akwai dabarun kasa don horar da mutane masu hazaka, tare da jami’o’i da kwalejoji kusan 3,200 suna daukar adadi masu shiga kashi 99.9 cikin dari.

Yunkurin da kasar Sin ta yi na rage fitar da iskar ‘Carbon’ ya sa aka mai da hankali kan kera motocin lantarki da masu amfani da makamashi mai tsafta, kamar iska da hasken rana.

kasar Sin tana tafiyar da tsarin tattalin arziki na dijital. A baya, jinkirin biyan haraji yana haifar da hukunci, amma a yau, ‘yan kasa za su iya biyan haraji ta hanyar amfani da wayoyin hannu da ID a cikin dakika guda, godiya ga samun damar intanet ta samar da miliyan 730 na masu amfani da intanet daga cikin al’umma biliyan 1.4.

Don tabbatar da samar da guraben ayyukan yi ga ‘yan kasar, kasar Sin na samar da guraben ayyukan yi miliyan 15 a duk shekara a dukkan bangarori, inda ta fitar da mutum miliyan 800 daga kangin talauci tsakanin shekarar 1979 zuwa 2020.

Yawan mutanen da suka tsufa, wadanda shekarunsu suka kai 60 zuwa sama, ya kai miliyan 310, wanda ke wakiltar kashi 18 cikin 100 na yawan jama’ar kasa.

Gwamnatin kasar Sin ta nuna rashin amincewa da cin hanci da rashawa, inda jam’iyya mai mulki da ‘yan adawa suka yi biyayya ga wannan ka’ida.

Masana sun yi nuni da cewa, idan kasar Sin da kasashe masu tasowa za su iya yin hadin gwiwa, to duniya za ta zama wuri mafi kyau.

Yayin wani taron kara wa juna sani na shugabannin kungiyoyin ‘yan jarida na kasashe abokan hadin gwiwa a fannin raya rayuwar al’umma, Mr. Wu Hao, mataimakin Daraktan Sashen Gudanarwa na Shirye-shiryen Horar da Kayayyakin Agaji na kasar Sin, ya bayyana cewa, “Za ku ci karo da hakikanin kasar Sin, al’adunta, jama’arta, da da kuma tarihinta.”

Bayan makonni biyu a cikin wannan kasa mai fadi da ban mamaki, hakika mun hadu da mutane, al’adunsu, salon rayuwarsu da tunaninsu. Mun dandana ainihin kasar Sin, kuma na same ta tana da ban sha’awa sosai.

Yayin da Mr Wu ya yi magana game da falsafa, akida, da ayyukan kasar Sin, ya bayyana a fili cewa yin aiki tare don samar da zaman lafiya wata muhimmiyar hanya ce ta ci gaba.

A kan tafiya zuwa zamani kuwa, kamar yadda Wang Yongzhong ya bayyana, wadannan mutane masu ban mamaki sun yi aiki tukuru don cimma irin wannan nasara.

Tun daga ranar farko da na isa kasar Sin, na lura da aikin gina sabbin layukan karkashin kasa na birnin Beijing.

Manufar shugaba di Jinping, da nufin cin gajiyar al’ummomin da ke fama da talauci a duniya, ya sanya kasar Sin a sahun gaba wajen girmamawa, da godiya, daga miliyoyin mutane a fadin Asiya, Oceania, Latin Amurka, Afirka, da Turai.

A yayin wata lacca da Mrs du Zhengyuan ta gabatar, an tattauna batun aiwatar da shirin Belt and Road Initiatibe (BRI). A cikin ‘yan shekarun nan, kasar Sin ta kasance kasa mafi saurin bunkasar tattalin arziki a duniya.

A gaskiya, ziyarar kwanaki uku da na kai Chongking, wata kwarewa ta musamman a cibiyar baje kolin kayayyaki ta kasa da kasa ta Chongking, kauyen Hero Bay, tare da tarurrukan da suka dace a rukunin kafofin watsa labaru na Chongking da cibiyar sadarwar kasa da kasa ta yammacin kasar Sin, ta nuna cewa kasar Sin na da kwarin gwiwar cimma nasarori a shekaru masu zuwa!

wannan babban aikin saka hannun jari na kayayyakin more rayuwa yana da nufin habaka hadin kai, kasuwanci, da sadarwa a cikin Eurasia, Latin Amurka, da Afirka.

kasar Sin tana goyon bayan gina tashoshin jiragen sama, tashoshin jiragen ruwa, na’urorin samar da wutar lantarki, gadoji, layin dogo, tituna, da hanyoyin sadarwar, tare da kokarin inganta dangantakar tattalin arziki da hadin gwiwa. Sakamakon wannan shiri dai al’ummar kasashen da suka ci moriyar wannan Shirin, wata irin baiwa ce ta Ubangiji.

Tun da yake ba zai yiwu a kawo kowa ya shaida ainihin kasar Sin ko kuma nuna sakamako da fa’ida a duniya ba, hujja mafi gamsarwa ta ta’allaka ne a cikin wadannan hujjoji da alkaluma da ba za a iya musantawa ba.

Ziyarar babbar ganuwa ta nuna irin girman da kasar Sin take da shi.

A al’adu da yawa, ana koya wa yara karatu da aiki tukuru don tara dukiya. Sabanin haka, al’adun kasar Sin sun sanya dabi’un da za su karfafa wa yara su koyi fasahohi masu kima don taimakawa wasu, da inganta al’umma, da ba da gudummawa ga ci gaban kasarsu.

Sakamakon wannan tunani da al’adu, jama’ar kasar Sin sun mayar da kasarsu ta asali ta zama kasa mai wadata.

Wani dan gajeren fim da farfesa Zhang Long ya gabatar, wanda ke baje kolin masu aikin sa kai wadanda suka yi aiki tukuru don mayar da hamadar Mu Us zuwa koriyar aljanna.

Nasarorin da kasar Sin ta samu, da shirin samar da hanya mai inganci, da gudummawar da take bayarwa ga kasashe da al’ummomi masu fama da talauci, da saurin bunkasuwar tattalin arzikinta, da al’adu da wayewar da take da su, darasi ne da ya kamata ‘yan Nijeriya da ‘yan Afirka su amince da su idan ana son ci gaba.

 


Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

ShareTweetSendShare
Previous Post

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3, Sun Sace 26 A Zamfara

Next Post

Gasar Wasanni Ta Kasa: FCT Ta Lallasa Borno Da Ci 4-1 A Wasan Farko

Related

Gwamna Nasir Ya Naɗa Sabbin Sakatarori Na Ƙananan Hukumomi 21 A Kebbi
Labarai

Gwamna Nasir Ya Naɗa Sabbin Sakatarori Na Ƙananan Hukumomi 21 A Kebbi

15 minutes ago
Kotu
Labarai

Kotu Ta Daure Wasu Mutane 3 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Mutum A Gidan Yarin Adamawa

2 hours ago
Zamfara
Manyan Labarai

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3, Sun Sace 26 A Zamfara

5 hours ago
Iyalan Sarkin Da Aka Kama Suna Neman Taimakon Kudin Fanso Shi Miliyan ₦50
Tsaro

Iyalan Sarkin Da Aka Kama Suna Neman Taimakon Kudin Fanso Shi Miliyan ₦50

7 hours ago
Gwamnan Kano Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Tsaro
Tsaro

Gwamnan Kano Ya Rantsar Da Sabon Kwamishinan Tsaro

8 hours ago
Akwai Kure A Maganar Gwamna Kan Kulawa Da Masu Rauni – Ƙungiyar Dattawan Zamfara
Tsaro

Akwai Kure A Maganar Gwamna Kan Kulawa Da Masu Rauni – Ƙungiyar Dattawan Zamfara

10 hours ago
Next Post
Gasar Wasanni Ta Kasa: FCT Ta Lallasa Borno Da Ci 4-1 A Wasan Farko

Gasar Wasanni Ta Kasa: FCT Ta Lallasa Borno Da Ci 4-1 A Wasan Farko

LABARAI MASU NASABA

Gwamna Nasir Ya Naɗa Sabbin Sakatarori Na Ƙananan Hukumomi 21 A Kebbi

Gwamna Nasir Ya Naɗa Sabbin Sakatarori Na Ƙananan Hukumomi 21 A Kebbi

May 19, 2025
Hadin Gwiwa Bisa Daidaito Da Girmama Juna Tsakanin Sin Da Amurka Zai Samar Da Moriyar Juna

Hadin Gwiwa Bisa Daidaito Da Girmama Juna Tsakanin Sin Da Amurka Zai Samar Da Moriyar Juna

May 19, 2025
Yankin Taiwan Ba Shi Da Iko Ko Hujjar Halartar Taron WHA

Yankin Taiwan Ba Shi Da Iko Ko Hujjar Halartar Taron WHA

May 19, 2025
Kotu

Kotu Ta Daure Wasu Mutane 3 Da Ake Zargi Da Kisan Wani Mutum A Gidan Yarin Adamawa

May 19, 2025
Xi Jinping Ya Ba Da Umurni Game Da Babban Shirin Shekaru Biyar-Biyar Na Bunkasa Tattalin Arziki Da Zamantakewar Kasar Sin Na 15

Xi Jinping Ya Ba Da Umurni Game Da Babban Shirin Shekaru Biyar-Biyar Na Bunkasa Tattalin Arziki Da Zamantakewar Kasar Sin Na 15

May 19, 2025
Sin Ta Cimma Nasarar Gwajin Jirgin Sama Samfurin AG600

Sin Ta Cimma Nasarar Gwajin Jirgin Sama Samfurin AG600

May 19, 2025
Gasar Wasanni Ta Kasa: FCT Ta Lallasa Borno Da Ci 4-1 A Wasan Farko

Gasar Wasanni Ta Kasa: FCT Ta Lallasa Borno Da Ci 4-1 A Wasan Farko

May 19, 2025
Fahimtar Hakikanin kasar Sin

Fahimtar Hakikanin kasar Sin

May 19, 2025
Zamfara

‘Yan Bindiga Sun Kashe Mutum 3, Sun Sace 26 A Zamfara

May 19, 2025
Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Bisa Daidaito A Afirilu

Tattalin Arzikin Sin Ya Bunkasa Bisa Daidaito A Afirilu

May 19, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.