• English
  • Business News
Monday, October 20, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [6]

by Nuhu Ubale Ibrahim
7 months ago
Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai

Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai

قَوْلُهُ عَلَيْهِ السَّلَامُ مُقَدَّمٌ عَلَى أَقْوَالِ النَّاسِ
Fassara:

“Maganar Manzon Allah (S.A.W) ita ake gabatarwa a kan magana mutane baki ɗaya “ Duba Kitãbu at-Tashīlu Li’ulūmi at-Tanzil [1/7].

Fashin Baƙi:

Wannan magana ta babban malami Ibnu Juzai Allah Ya yi masa rahama ƙa’ida ce da tushenta yake da dalilai daga Alƙur’ani da Hadisi, kuma malamai da dama sun jaddada muhimmancinta da wajabcin aiki da ita a fili da ɓoye.

  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [4]
  • Fa’ida Daga Tafsirin Alƙur’ani Na Ibnu Juzai [5]

Allah Ta’ala Yana cewa:” Ya ku mummunai! Ku yu ɗa’a ga Allah, kuma ku yi ɗa’a ga Manzo da kuma majiɓinta lamarinku. Idan kun yi jayayya a kan wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzonsa in kun kasance kun yi imani da Allah da ranar ƙarshe. Wannan shi ne mafi alheri, kuma mafi kyawun makoma” Suratun Nisã’i aya ta 59.

LABARAI MASU NASABA

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Wannan aya tana nuna cewa idan aka sami saɓani, to dole ne a mayar da al’amari zuwa ga Allah da Manzonsa, wato Alƙur’ani da Sunna. Allah Ta’ala Ya ƙara cewa:” Kuma abin da Manzo ya ba ku sai ku karɓe shi, abin kuma da ya hana ku sai ku hanu. Ku kuma kiyaye dokokin Allah, Lalle Allah Mai tsananin uƙuba ne.” Suratul Hashri aya ta 7. Manzon Allah (S.A.W) ya ce: “Duk abin da na hane ku, to ku nisance shi; kuma abin da na umarce ku, to ku aikata shi gwargwadon iyawarku.” Bukhari ne ya ruwaito [#7288] da Muslim[#1337]. Wannan hadisi yana nuna cewa dole ne a bi umurnin Annabi (S.A.W) kuma a nisanci abin da ya hana.

Maganganun Malamai:

Banyan malaman Musulunci kuma jagorin shiriya sun bayyana maganar Manzon Rahama(S.A.W) ita ce ta fi cancanta abi a kan maganar mutane baki ɗaya. Ga maganar wasu daga cikinsu:

Imam Abu Hanifa Allah Ya yi masa rahama yana cewa:” Idan hadisi ya inganta, to shi ne Mazahabata” Duba Ibnu Abidin; al-Hãshiyatu [1/63]. Wannan yana nuna cewa Imam Abu Hanifa yana fifita hadisin Annabi (S.A.W) kan ra’ayinsa ko ijtihadinsa.

Imam Malik Allah Ya yi masa rahama shi kuma cewa ya yi:” Ni mutum ne, ina yin daidai kuma ina kuskure, ku duba ra’ayina, duk wanda ya dace da Alƙur’ani da Sunna, to ku riƙe shi, duk kuma wanda ya saɓa wa Alƙur’ani da Sunna, to ku bar shi.” Duba Ibnu Abdilbarri; Jãmi’u Bayãnil ilmi [2/32]. Imam Malik yana nuni da Alƙur’ani da Sunnar Annabi (S.A.W) su ne abin gabatarwa a bisa maganarsa.

Imam ash-Shafi’i Allah Ya yi masa rahama shi kuma cewa ya yi:”Idan hadisi ya inganta, to shi ne Mazahabata” Duba an-Nawawi; al-Majmū’u [1/63]. Wannan yana nuna cewa Imam ash- Shafi’i yana fifita hadisin Annabi a kan ra’ayinsa ko ijtihadinsa.

Imam Ahmad ɗan Hanbal Allah Ya yi masa rahama cewa ya yi:” Duk wanda ya ƙi karɓar Hadisin Manzon Allah Sallallahu alaihi wa alihi wa sallam, to yana gaɓar halaka” Duba Ibnul Jauzi; al-Manãƙibu [shafi na 182].
Wannan yana nuna cewa Imam Ahmad yana karɓar koyarwar Annabi (S.A.W) fiye da ra’ayoyin mutane, kuma ƙin karɓar hadisi halaka ne.

Maganar Ibn Juzai tana tabbatar da cewa maganar Annabi Muhammad (S.A.W) ita ce ake ba wa muhimmanci a kan maganar sauran mutane, kuma ita ce shiriya, saɓa mata kuma halaka ne da ɓata. Allah Ya datar da mu da bin Annabi (S.A.W) a fai da ɓoye. Amin.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

gombe
Ilimi

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma
Ilimi

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
ASUU
Ilimi

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025
Next Post
Ranar Mata Ta Duniya: Kalubalen Da Mata Ke Fuskanta A Siyasar Nijeriya

Ranar Mata Ta Duniya: Kalubalen Da Mata Ke Fuskanta A Siyasar Nijeriya

LABARAI MASU NASABA

Hukumar EFCC Ta Tsare Wasu Jami’anta 10 Bisa Zargin Karkatar Da Kayan Aiki

EFCC Ta Ƙwato Kadarorin Naira Biliyan 500 A Ƙarƙashin Gwamnatin Tinubu – Shettima

October 20, 2025
Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara

Kano Pillars Ta Dakatar Da Manyan Masu Horas Da ‘Yan Wasanta Saboda Rashin Nasara

October 20, 2025
Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

Bayan Kauce Hanya, Jirgi Ya Afka Cikin Teku A Hong Kong 

October 20, 2025
Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja

Jami’an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar #FreeNnamdiKanuNow A Abuja

October 20, 2025
Wani Mai Taɓin Hankali Ya Kashe Mutum 1, Ya Raunata 3 A Taraba

Wani Mai Taɓin Hankali Ya Kashe Mutum 1, Ya Raunata 3 A Taraba

October 20, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kama Alburusai 400 A Delta

October 20, 2025
Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

Kano Derby: Barau FC Ta Doke Kano Pillars A Karon Farko A Tarihin Gamuwarsu

October 19, 2025
Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

Binciken CGTN: An Fitar Da Sakamakon Jin Ra’ayin Jama’a Dangane Da Cikakken Zama Na 4 Na Kwamitin Kolin JKS Na 20

October 19, 2025
Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

Arewa Ta Samu Kashi 56% Na Muƙaman Gwamnatin Tinubu — Shugaban FCC

October 19, 2025
Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

Xi Jinping Ya Mika Sakon Taya Cheng Li-wun Murnar Zama Shugabar Jam’iyyar KMT Ta Kasar Sin

October 19, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.