Ibnu Juzai Allah Ya yi masa rahama yana cewa:
“الحَسَدُ خُلُقٌ مَذْمُومٌ طَبْعًا وَشَرْعًا.”
Fassara:
” Hassada mummunar ɗabi’a ce, a ɗabi’a da shari’a.”
Fashin Baƙi:
Ibnu Juzai al-Kalbi Allah Ya yi masa ranama yan nuna mana munin hassada ta fuska biyu:
1. A Ɗabi’a: Hassada tana haifar da cutar zuciya, wadda ke hana mutum farin ciki da jin daɗin rayuwa, kuma tana sa mai yin ta ya zama mai mugun hali, da ƙoƙarin ganin wani ya faɗi ko ya rasa abin da ya samu. A al’ada, mutane suna ƙin mai hassada saboda halayensa na rashin son alheri ga mutane da kuma fatan sharri a gare su.
2. A Shari’a: A cikin Alƙur’ani, Allah ya yi umurni da a nemi tsari a wurinsa daga hassadar mahassadi, inda Ya ce:” Ka ce:” Ina neman tsari da Ubangijin asuba. Daga sharrin abin da Ya halitta. Da kuma sharrin dare idan ya lulluɓe da duhu. Da kuma sharrin mata masu tofi a cikin ƙulle-ƙulle. Da kumma sharrin mahassadi yayin da ya yi hassada.” Suratul Falaƙ aya ta 1-5. Manzon Allah (ﷺ) ya ce: “Kada ku yi hassada da juna…” Muslim ne ya ruwaito [#2563].
Hassada tana iya kai mutum ga saɓawa Allah, kamar yadda Shaiɗan ya ƙi yin sujada ga Adam saboda kishi da hassada. Hassada tana haifar da cin amanar ‘yan’uwa, da munafunci, da karya. Hassada tana cutar da mai yin ta fiye da wanda ake yi wa. A ɗabi’a, tana hana kwanciyar hankali, a shari’a kuwa tana kai mutum ga zunubi. Maimakon yin hassada, Musulumi ya kamata ya roƙi Allah ya ba shi alheri kamar yadda Ya ba wa waninsa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp