Ibnu Juzai a-Kalbi Allah Ya yi masa rahama yana cewa:
وَقَالَ بَعْضُ العُلَمَاءِ: الحَسَدُ أَوَّلُ مَعْصِيَةٍ عُصِيَ اللَّهُ بِهَا فِي السَّمَاءِ وَالأَرْضِ، أَمَّا فِي السَّمَاءِ فَحَسَدُ إِبْلِيسَ لِآدَمَ، وَأَمَّا فِي الأَرْضِ فَقَتْلُ قَابِيلَ لِأَخِيهِ هَابِيلَ بِسَبَبِ الحَسَدِ.
Fassara:
“Wasu malamai sun ce: Hassada ita ce laifi na farko da aka yi wa Allah a sama da ƙasa. Amma a sama, Iblis ne ya yi wa Adam hassada, a ƙasa kuma, Ƙabila ne ya kashe ɗan’uwansa Habila saboda hassada.” Duba Kitãbu at-Tashīlu Li’ulūmi at-Tanzil [4/226]
Fashin Baƙi:
Maganar da Ibn Juzai ya kawo tana nuna cewa hassada tana daga cikin manyan laifuka na farko da aka yi wa Allah, kuma tana da mummunan tasiri a rayuwar mutum da zamantakewarsa. Ga bayani dalla-dalla:
1. Hassadar Iblis ga Annabi Adam (A.S) a Sama: Lokacin da Allah ya halicci annabi Adam (A.S.) kuma ya ba shi girma, yana da ilimi da matsayi mafi daraja fiye da sauran halittu, Allah ya umurci mala’iku su yi masa sujada. Dukkan mala’iku sun yi biyayya, amma Iblis ya ƙi, yana mai girman kai da hassada ga annabi Adam (A.S).
Dalilin hassadar Iblis ga Annabi Adam: Ya ga cewa Allah ya fifita Adam a kansa. Ya raina Adam saboda an halicce shi daga ƙasa, shi kuma daga wuta. Ya ji haushin cewa zai rasa matsayinsa a wajen Allah.
Sakamakon wannan hassadar, sai Iblis ya zama la’ananne, kuma Allah ya kore shi daga rahama. Wannan yana nuna cewa hassada na iya kai mutum ga yin tawaye ga tsarin Allah wanda hakan halaka ne da taɓewa da hasara a duniya da lahira.
Hassadar Ƙabila ga Habila a Ƙasa: A lokacin Annabi Adam (A.S.), Allah ya karɓi hadayar Habila, amma bai karɓi ta Ƙabila ba. Wannan ya haddasa hassada a zuciyar Ƙabila har ta kai shi ga yin kisan kai na farko a duniya.
Dalilin hassadar Kabila ga Habila: Ya ga cewa Allah ya karɓi hadayar Habila, ba tashi ba. Ya ji haushin cewa Habila na da falala fiye da shi. Bai yarda da hukuncin Allah ba, sai ya lallaɓa har ya kashe ɗan’uwansa.
Sakamakon haka, Ƙabila ya kasance cikin nadama da tozarta, kuma ya zama wanda ya fara kisan kai a duniya.
Darasin da za a koya daga wannan Magana:
1. Hassada tana kai mutum ga zunubi: kamar yadda Iblis ya yi tawaye, Kabila kuma ya kashe ɗan’uwansa.
2. Allah ne ke bayar da daraja: Domin Ya fifita Adam da Habila, ba don wani abu ba sai hikimarsa da falalarsa.
3. Ya kamata mutum ya yarda da ƙaddarar Allah: Domin da Iblis ya yarda da ƙaddara da bai ƙi yin sujjada ga Annabi Adama AS.S) ba.
4. Hassada tana hana mutum albarka: Iblis ya rasa matsayinsa, Ƙabila kuma ya rasa ɗan’uwansa kuma ya shiga baƙin ciki.
A ƙarshe, wannan magana tana ƙarfafa mu, da mu guji hassada, mu gamsu da abin da Allah ya ba mu, domin tana iya rushe duk wata kyakkyawar dangantaka da haifar da halaka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp