Babban lauya kuma mai kare haƙƙin ɗan Adam, Femi Falana (SAN), ya bai wa ƴan Nijeriya shawara da su kai Gwamnatin Tarayya ƙara don neman a mayar musu da kuɗin fansar da suka biya yayin da aka yi garkuwa da ƴan uwansu. Ya ce gwamnatin ta kasa sauke babban nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata na kare rayuka da dukiyoyin ƴan ƙasa.
Falana ya yi wannan jawabi ne a lokacin buɗe sabuwar shekarar Shari’a ta Tsangayar Shari’a ta Jami’ar Yakubu Gowon da ke Abuja. Ya ce yawaitar garkuwa da mutane a sassan ƙasar nan ya nuna gazawar gwamnati wajen tabbatar da kariya kamar yadda kundin tsarin mulki da Yarjejeniyar Afrika kan Haƙƙin Dan Adam suka tanada. Ya kuma soki bambancin yadda hukumomi ke tunkarar lamarin, yana mai cewa ana hanzari ne idan manyan mutane aka sace, amma an bar talakawa cikin tsoro da halin ƙaƙa-niki-ka-yi.
- Falana Ya Kai Karar Gwamnatin Tarayya Da Jihohi Kan Yara Da Ba Su Zuwa Makaranta
- Tsauraran Manufofin Tattalin Arziƙin Tinubu Ya Ƙara Yawan Matalauta – Falana
Falana ya jaddada cewa kai gwamnati kotu zai taimaka wajen kare haƙƙin waɗanda suka biya kuɗin fansa, tare da matsa wa gwamnati ta inganta tsaro cikin gaggawa. Sabon rahoton Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ya nuna cewa ƴan Nijeriya sun biya Naira Tiriliyan 2.23 a matsayin kuɗin fansa tsakanin Mayu 2023 zuwa Afrilu 2024. Rahoton Crime Experience and Security Perception Survey (CESPS) na 2024 ma ya nuna cewa fiye da mutum miliyan 2.2 an yi garkuwa da su a wannan lokaci, tare da matsakaicin kuɗin fansa na kusan ₦2.7m ga kowane mutum.
A cewar masana tsaro, garkuwa da mutane ya koma kasuwancin da ke samar da riba ga miyagu, lamarin da ke buƙatar tsauraran matakai daga gwamnati tare da ingantaccen tsari da haɗin gwuiwar jami’an tsaro.













