An gudanar da wani gagarumin biki a ofishin jakadancin Faransa, da ke Abuja don gabatar da dabarun binciken da hukumar raya ƙasashe ta Faransa (AFD), ta ɗauki nauyin ƙarƙashin kulawar wata cibiya mai suna “Semmaris”, da zummar zamanantar da kasuwannin hada-hadar kayan noma a Nijeriya.
Tsare-tsaren sun mayar da hankali ne kan samar da wasu muhimman hanyoyi uku a Nijeriya, tare da haɗa yankunan karkara da manyan birane kamar su jihohin Kano zuwa Kaduna, da Legas zuwa Ogun da Ibadan, da ma garin Onitsha zuwa Fatakwal, don rage asarar bayan girbi tare da inganta safarar amfanin gona da bunƙasa samar da abinci ta yadda za a samar da ayyukan yi.
- An Bukaci Gwamnain Tarayya Ta Sake Inganta Harkokin Amfanin Gona
- Gudunmawar Da Sin Take Bayarwa Wajen Tabbatar Da Wadatar Abinci A Duniya
Yayin da wakilan cibiyar Semmaris da AFD, ke miƙa rahoton binciken suka yi, ƙaramin ministan noma da samar da abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, ya bayyana gamsuwarsa da shirin tare da jaddada muhimmancinsa wajen ci gaban Nijeriya, da bunƙasa ayyukan noma da samar da abinci wanda ya ce ya yi dai-dai da wani shirin gwamnati haɗin gwuiwa da Bankin duniya.
Ministan ya yaba da hadin gwuiwar tsakanin Faransa da Nijeriya inda ya jaddada muhimmiyar rawar da noma ke takawa wajen bunkasar tattalin arziki da samar da ayyukan yi wanda ya ce gwamnatin Nijeriya za ta shirin muhimmanci yadda ake buƙata.
Semmaris wanda kamfanin Faransa, ne da ke kula da kasuwar sayar da kayayyaki na Paris da Rungis, ɗaya ne daga cikin manyan masu harƙallar kasuwancin kayan abinci a duniya kuma ya sahara wajen safarar amfanin gonaki da ajiyarsu, inda ake sa ran wannan haɗin gwuiwar tsakanin za ta ƙunshi wasu kamfanoni na Faransa da yawa, tare da amfani da ƙwarewarsu wajen inganta ayyuka da kasuwancin kayan amfanin gona.
Aikin ya haɗa da zuba hannun jari wajen zamanantar da hanyoyin samar da kayayyaki da bunƙasa wuraren ajiya da ababen more rayuwa na kasuwa, da kuma himma wajen ƙarfafawa manoma da masu gudanar da kasuwanci damar gogayya a kasuwannin duniya.