A karon farko tun bayan soma yaki tsakanin Rasha da Ukraine, farashin alkama a kasuwannin duniya ya sauko sosai.
Dukkan kasashen sun sanya hannu kan yarjejeniya a jiya Juma’a, inda aka amince cewa za a ci gaba da fitar da hatsi ta tekun Black Sea wanda Rasha ta toshe tsawon watanni.
- NIS Ta Ƙaddamar Da Hukumar Gudanarwar Asusun Kula Da Baƙin Haure
- Saudiyya Ta Kama Wanda Ya Shigar Da Wanda Ba Musulmi Ba Cikin Makkah
Rebecca Grin Span, wadda babbar sakatariya a Majalisar Dinkin Duniya ce kan cinikayya da kuma raya kasa na da cikin jagorori a yarjejeniyar da aka cimma.
Ta ce wannan yarjejeniya ce kwarai da gaske da ta shafi duniya, saboda za ta shafi miliyoyin mutane musamman wadanda ke a kasashe masu tasowa.
Shugaban Ukraine Volodymyr Zekensky, ya ce fitar da tan miliyan 20 na hatsi zai taimaka wajen kauce wa fadawa gagarumar matsalar karancin abinci a duniya.