Yayin da ake ci gaba da nuna damuwa kan tashin farashin man fetur, farashin gas din girki ya hau zuwa Naira 1,500 kan kowane kilo.
Wannan karin ya zo ne a daidai lokacin da ‘yan Nijeriya ke ci gaba da kokawa da tsadar man fetur, lamarin da ke kara jefa maginta cikin rudani kan amfani da gas wajen girki a kullum.
- Dan Nijeriya Ya Samu Kyautar Dala 600 Bayan Lashe Gasar Mr. Olympia A Amurka
- Haɗama, Son Kai Da Jahilci Ne Sanadin Wahala A Nijeriya – Obasanjo
Manajan Darakta kuma Babban Jami’in kamfanin NIPCO Plc, Suresh Kumar, ya bayyana fatansa na rage farashin a nan kusa, inda ya ce, da zarar Matatar Dangote ta kama aiki gadan-gadan, za a rage yawan shigowa da gas din daga kasashen waje.
Ya bayyana cewa, sama da kashi 60 cikin 100 na iskar gas a Nijeriya a halin yanzu ana shigo da shi ne daga kasashen waje, wanda ke haifar da tsadar iskar gas din.
Wani bincike da aka gudanar a baya-bayan nan ya tabbatar da cewa, farashin iskar gas a jihohin Ogun da Legas ya kai Naira 1,500 kan kowane kilo, yayin da a Abuja kuma, farashin cika kwatankwacin kilo 12.5 na tukunyar gas ya karu da kashi 41.6 cikin 100, wanda ya kai Naira 17,000 wanda a baya ya ke akan Naira 12,000.
A watan Agusta, Karamin Ministan Albarkatun Man Fetur (Gas), Ekperikpe Ekpo, ya sha alwashin magance hauhawar farashin iskar gas, inda ya yi alkawarin hada kai da hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki.