Farashin gas mai nauyin kilogiram 5 ya karu daga N4,474.48 a watan Satumba zuwa N4,483.75 a watan Oktoba, wanda ya tashin zuwa kashi 0.21%.
Wannan na dauke je cikin wata sanarwa da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta bayyana a Abuja.
- Ziyarar Xi Jinping Ta Taimakawa Duniya Kara Fahimtar Kasar Sin
- ‘Yansanda Sun Ceto Matafiya 76 Daga Hannun ‘Yan Bindiga A Kaduna
A cikin shekara guda, an samu karin kashi 70.62 bisa dari daga N2,627.94 a watan Oktoban 2021 zuwa N4,483.75 a watan Oktoban 2022, in ji NBS.
A nazarin bayanan rahoton ya nuna cewa Jihar Kwara ta samu matsakaicin farashin a kan N4,955 kan kilo 5 na gas, sai Neja ta biyo baya a kan N4,950 sai Adamawa kan N4,940.29.
Rahoton ya bayyana cewa Abia ta samu mafi karancin farashi a kan N4,045.45, sai Kano da Delta kan N4,100 da kuma N4,139.29, bi da bi.
Bincike ya nuna cewa Arewa ta Tsakiya ta samu matsakaicin farashin kan N4,726.07 na gas mai nauyin kilogiram 5, sai kuma Arewa maso Gabas a kan N4,577.86.
A yankin Kudu-maso-Kudu an samu mafi karancin farashi a kan N4,275.92.
NBS ta kuma bayyana a cikin rahoton cewa matsakaicin farashin gas mai nauyin kilogiram 12.5 ya karu daga N9,906.44 a watan Satumba zuwa N10,050.53 a watan Oktoba, wanda hakan ke nuna karuwar kashi 1.45 a duk wata.
Ta kara da cewa a duk shekara, ana samun karin kashi 51.4 daga N6,638.27 a watan Oktoban 2021 zuwa N10,050.53 a watan Oktoban 2022.
A Kuros Riba kuwa, an samu matsakaicin farashin kan N10,986.11 na gas mai nauyin kilogiram 12.5, sai Jihar Oyo a kan N10,826.56 sai Kogi a kan N10,783.33.
Rahotan ya bayyana cewa, an samu mafi karancin farashi a Yobe kan N8,533.33, sai Sakkwato da Katsina kan N9,100.00 da kuma N9,202.86.