Hukumar Kiddiga ta Kasa ta bayyana cewa farashin kalanzir da gas ya karu da kashi 88 cikin 100 a cikin shekara daya.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wani rahoto da ta fitar mai taken ya kamata a yi duba da hauhawar farashin kalanzir’, inda farashin kalanzir ya karo da kashi 86.94 a cikin shekara daya.
- Farashin Gas Din Girki Ya Kara Yin Tashin Gwauron Zabi — NBS
- An Shigo Da Madarar Naira Biliyan 27 Nijeriya Cikin Wata Uku – NBS
Haka kuma rahoton ya bayyana cewa lita daya na kalanzir yana karuwa a duk wata da kashi 15.21 a watan Mayun 2022, wanda ya karu da naira 589.82 a watan Afrilun 2022, yayin da ya karu da naira 679.54 a watan Mayun 2022.
Rahoton ya nuna cewa Jihar Inugu ce ta fi samun hauhawar farashin kalanzir a watan Mayun 2022, inda aka sami karuwan naira 868.75, sai kuma Jihar Ebonyi da aka samu Karin naira 861.11, da kuma Jihar Imo da aka samu karuwar naira 801.67.
A hannu daya kuma, jihar da ta fi samun karancin hawar farashin kalanzir kuma ita ce Jihar Beyelsa wand aka samu na naira 558.06, sai kuma Jihar Yobe da ke da naira 601.39 da kuma Jihar Nasarawa da ke Karin naira 603.33.
Haka kuma hukumar ta ce farashin gas na girki ya karu da kashi 89.28, wanda ya karu da naira 2071.69 a watan Mayun 2022.