Farashin kayayyakin abinci na cigaba da sauka sosai a jihohin Borno, Yobe da Adamawa, a cewar wani bincike da Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya gudanar a manyan kasuwanni.
Rahoton ya nuna cewa farashin shinkafa, masara, wake, gero, barkono, taliya da man girki ya ragu idan aka kwatanta da watannin baya. A Kasuwar Monday ta Maiduguri, buhun shinkafa na kilo 50 da ake sayarwa kan N78,000 zuwa N82,000 yanzu yana tsakanin N64,000 zuwa N65,000, yayin da masara ta koma N40,000 zuwa N45,000 daga N60,000 zuwa N65,000 da ake sayarwa a baya. Haka ma barkono, wake, gero da dawa sun yi sauƙi a kasuwanni daban-daban na Maiduguri, Damaturu da Yola.
- ‘Yansanda Sun Tsaurara Tsaron Iyakokin Kano Bayan Hare-haren ‘Yan Bindiga
- An Yanke Wa Tsohuwar Shugabar Bangladesh Hukuncin Kisa
Masu sayar da hatsi da kayan marmari sun danganta sauƙin farashin da yawaitar amfanin gona daga manoma da kuma ƙarin ingancin tsaro da ya bai wa al’umma damar komawa gonaki. Wasu ’yan kasuwa sun ce sauyin manufofin gwamnati musamman kan shigo da hatsi ya taka rawa wajen cike kasuwa da kaya, abin da ya karya farashi.
A Damaturu, farashin mudun shinkafa ya ragu daga N5,000 zuwa N2,500, yayin da wake, masara da gero suma suka sauka fiye da rabin tsohon farashinsu. Masana tattalin arziki sun ce yawaitar shigo da hatsi kamar shinkafa da alkama ya taimaka wajen rage tsadar abinci da ake fama da ita a watannin baya.














