Farashin kayayyaki ya karu zuwa kashi 20.52 cikin 100 a watan Agusta, wanda hakan ya sa farashin kayan abinci ya yi tashin gwauron zabi.
Yawan hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya haura kashi 20 cikin 100 a watan Agusta yayin da farashin kayayyaki da na ayyuka ke ci gaba da hauhawa.
- Nijeriya Da Morocco Za Su Sanya Hannu Kan Kulla Yarjejeniyar Aikin Bututun Iskar Gas
- Da Dumi-dumi: Shugaban Hukumar ‘Yansanda, Musiliu Smith Ya Yi Murabus
Sabbin alkaluman hauhawar farashin kaya da Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS), ta fitar ya nuna cewar ya karu zuwa kashi 20.52 cikin 100 daga kashi 19.64 a cikin 100 a watan Yulin 2022.
Hauhawr farashin kayan abinci ya na ci gaba da tashi tun daga watan Oktoban 2005 lokacin da ya kai kashi 24.56 cikin dari, wanda ya karu zuwa kashi 23.12 cikin dari daga kashi 22.02 cikin dari wanda ya kasance a watan Yuli.
Musamman hauhawar farashin kayan abinci ya samo asali ne sakamakon karin farashin Biredi da hatsi da kayan abinci da dankali da dawa da sauran kayayyaki masarufi da nama da mai da kifi.
A duk wata, hauhawar farashin kayan abinci ya kan daidaita da kashi 1.98, idan aka kwatanta da kashi 2.04 da watan da ya gabata.
Kididdigar farashin kayan masarufi da NBS ta fitar ta nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki a cikin watan Agusta na wannan shekara ya karu zuwa kashi 20.52, ya ninku zuwa kashi 3.52 cikin dari idan aka kwatanta da adadin da aka samu a watan Agustan 2021, wanda ya kai kashi 17.01 cikin dari.
Haka zalika, an samu karuwar mafi girman farashin iskar gas, man fetur mai da jigilar fasinja a hanya da jigilar fasinja ta jirgin sama.
Abubuwa na kara tsamari a Nijeriya, inda mutane da dama musamman talakawa ke Allah wadai da halin da ake ciki.