Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta bayyana cewa ƙimar hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ta sauka zuwa kashi 21.88% a watan Yuli 2025, daga kashi 22.22% da aka samu a watan Yuni 2025. Wannan na nuni da raguwa da kashi 0.34% idan aka kwatanta da watan da ya gabata.
Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin abinci na shekara-shekara a watan Yuli 2025 ya kai kashi 22.74%, wanda ya ragu da maki 16.79% idan aka kwatanta da kashi 39.53% da aka samu a Yulin 2024. NBS ta danganta wannan raguwa mai yawa da sauyin shekarar wajen lissafi.
- Hauhawar Farashin Kayayyaki Ya Kai Kashi 34.80 A Disamban 2024 – NBS
- Manzon Allah (SAW) Zai Cika Shekara 1,500 Da Haihuwa A Shekarar Nan (6)
A kan lissafin wata-wata, hauhawar farashin abinci a watan Yuli 2025 ya tsaya a kashi 3.12%, raguwa da kashi 0.14% daga kashi 3.25% na watan Yuni 2025. Hukumar ta ce hakan ya samo asali ne daga saukar farashin man gyaɗa, da wake fari, da shinkafar gida, da masara, da fulawa, da dawa, da alkama da sauran su.
Sai dai a fannin hauhawar farashin gaba ɗaya, rahoton ya nuna cewa a watan Yuli 2025 an samu ƙarin kashi 1.99% idan aka kwatanta da kashi 1.68% na watan Yuni 2025, ma’ana ƙimar hauhawar farashin wata-wata da ta fi ta watan da ya gabata.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp