Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta sanar da cewa rahoton hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya sauka zuwa kashi 22.22% a watan Yuni 2025, ƙasa da 22.97% da aka samu a watan Mayu.
Rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin abinci ma ya ragu zuwa 21.97% a cikin shekara guda, wanda ke nuna saukar kashi 18.90% idan aka kwatanta da rahoton Yuni 2024 da ya kasance 40.87%. Hukumar ta ce sauyin gwajin shekara (base year) ne ya taimaka wajen saukar alkaluman.
- Ma’aikatar Kasuwanci Ta Sin Ta Kara Kamfanoni 8 Na Yankin Taiwan Cikin Jerin Wadanda Aka Takaita Sayar Musu Kayayyaki
- ‘Yansanda Sun Damke Mutum Shida Kan Kisan Da Aka Yi A Kasuwar Abuja
Sai dai a wata-wata, hauhawar farashin abinci ya ƙaru zuwa 3.25% a Yuni, daga 2.19% da aka samu a Mayu. Wannan ƙarin ya samo asali ne daga tsadar kayan abinci kamar wake (danye), da tattasai, da busasshen kifi, da naman dabbobi.
Hakanan, matsakaicin hauhawar farashin kayayyaki cikin shekara guda ya sauka zuwa 26.58% a Yuni 2025 daga 30.00% a Yuni 2024. Wannan sauyin na nuna raguwar hauhawar farashi duk da ƙaruwar kuɗin farashi a wasu watanni na baya-bayan nan.
A wasu sassan, hauhawar farashi a birane ya kai 22.72% a Yuni, ƙasa da 36.55% da aka samu a bara. A karkara kuma, an samu 20.85%, wanda ya ragu da kashi 11.24% idan aka kwatanta da Yuni 2024. Wannan na nuni da rage hargitsi a farashin kayayyaki duka a birane da ƙauyuka.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp