Hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya karu zuwa kashi 27.33 a watan Oktoba daga kashi 26.72 cikin 100 a watan Satumban 2023.
Hukumar kididdiga ta kasa (NBS), ta bayyana hakan a cikin rahotonta na kididdigar farashin kayayyaki da ta fitar a ranar Laraba.
- Ranar ‘Yancin Kai: Tinubu Ya Bar Saudiyya Zuwa Guinea Bissau
- Ribadu Ya Bukaci NLC Ta Janye Yajin Aiki, Ya Yi Allah Wadai Da Cin Zarafin Da Aka Yi Wa Ajaero
Adadin na watan Oktoba ya nuna samun karin maki 0.61 cikin 100 idan aka kwatanta da watan Satumban 2023.
Bugu da kari, a kowace shekara, farashi ya kan kai maki 6.24 cikin 100.
NBS ta bayyana cewa hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya ya kai kashi 29.29 cikin 100.
Har ila yau, rahoton ya nuna cewa hauhawar farashin kayan abinci ya karu zuwa kashi 31.52 cikin dari, inda ya karu da maki 7.80 kuma shi ne mafi girma idan aka kwatanta da kashi 23.72 da aka samu a watan Oktoban 2022.
Alkaluman sun nuna cewa wannan shi ne karo na 10 da ake ci gaba da samun hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya.
Wannan dai na zuwa bayan cire tallafin man fetur tare da wasu tsare-tsare da gwamnatin shugaba Tinubu ta kaddamar tun bayan kama mulki.
Hakan ya sanya a baya-bayan nan kungiyoyin kwadago na NLC da TUC suka yi yunkurin shiga yajin aiki.