Farashin man fetur a Nijeriya ya sake tashi, inda gidajen mai a Jihar Legas suka ƙara farashin lita daga Naira 860 zuwa Naira 930.
A Abuja da manyan biranen Arewa, ana sayar da litar tsakanin Naira 950 zuwa Naira 970, wanda ya nuna an samu ƙarin Naira 70 zuwa Naira 90.
- Ana Share Fagen Gudanar Bikin Baje Kolin Kayayyakin Da Ake Shigar Da Su Kasar Sin Yadda Ya Kamata
- Mutane Biyu Sun Mutu, 20 Sun Jikkata A Yamutsin Filin Idi A Gombe
Ƙarin farashin na da nasaba da rikicin da ke tsakanin Matatar Dangote da Kamfanin NNPCL kan sayar da ɗanyen mai.
Matatar Dangote kwanan nan ta bayyana cewa ba za ta sake sayar da mai da Naira ba, saboda matsalolin samun ɗanyen mai a cikin gida.
Wannan matakin ya haddasa tangarɗar samar da mai, wanda ya tilasta wa ‘yan kasuwa ƙara farashi.
Wasu gidajen na ‘yan kasuwa ma sun bi sahu wajen ƙara farashi, wanda hakan ya ƙara jefa ‘yan Nijeriya cikin matsin tattalin arziƙi.
A halin yanzu, hauhawar farashin man fetur na nufin za a ƙara kudin sufuri da kuma farashin kayan masarufi, wanda zai ƙara jefa al’umma cikin kunci.
Masana harkar man fetur sun yi gargaɗin cewa, idan ba a magance rikicin da wuri ba, farashin mai na iya haura Naira 1,000 a wasu yankuna.
Gwamnatin Tarayya ta taɓa bayar da umarni cewa a sayar da ɗanyen mai ga matatun cikin gida da Naira domin daidaita farashin mai, amma yarjejeniyar ta ƙare a watan Maris 2025.
A halin yanzu, ana ci gaba da tattaunawa kan sabuwar yarjejeniya.
A yayin da wannan rikici ke ci gaba, ‘yan Nijeriya na fama da illolinsa.
An fara samun dogayen layukan a wasu yankuna a gidajen mai, sannan ‘yan kasuwa da ke amfani da janareta don samar da wutar lantarki na ƙara kokawa kan tsadar man.
Mutane da dama na kira ga gwamnati da ta gaggauta ɗaukar mataki domin shawo kan matsalar kafin ta ƙara ta’azzara.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp