Hukumar kididdiga ta kasa (NBS), ta fitar da rahoton watan Mayun 2024, inda ta ce farashin man fetur a Jihar Jigawa, ya kai Naira 937 kan kowace lita, wanda shi ne farashi mafi tsada da aka samu a fadin kasar nan.
Hauhawar farashin na cikin sabon rahoton NBS, game da farashin man fetur a watan Mayun 2024.
- Sauya Fasalin Dimokuradiyyar Afirka: Lokaci Ya Yi Da Za Mu Yada Kwallon Mangwaro Mu Huta Da Kuda
- Mutane 20 Sun Mutu, 52 Sun Ji Rauni A Harin Bam A Borno – DHQ
Karin farashin man fetur ya biyo bayan cire tallafin man fetur da shugaba Bola Tinubu ya yi a ranar 29 ga Mayu, 2023.
Matsakaicin farashin man fetur a watan Mayun 2024 ya kasance Naira 769.62, wanda ya kai kashi 223.21.
Jihar Jigawa ta fuskanci farashi man fetur mafi tsada a kan Naira 937.50, sai jihohin Ondo da Benue da ake sayar da fetur din a kan Naira 882.67 da Naira 882.22.
Inda da aka samu mafi karancin farashi na man fetur su ne jihohin Legas, Neja, da Kwara a kan Naira 636.80, Naira 642.16 da kuma Naira 645.15.
Yankin Arewa Maso Yamma su ne ‘yan tsakiya, inda aka samu farashin man fetur a kan Naira 845.26, yayin da yankin Arewa ta Tsakiya suka samu farashin a kan Naira 695.04.
Cire tallafin man fetur ya haifar da hauhawar farashin kayayyaki zuwa 33.95% a watan Mayu, tare da hauhawar farashin kayan abinci a kashi 40%.
Duk da karin farashin na man fetur, Kamfanin Man Fetur na Nijeriya (NNPCL) ya ci gaba da sayar da fetur a kan Naira 568 kan kowace lita.