Yayin da babbar Sallah ke gabatowa, farashin dabbobin hadaya a jihar Kaduna ya yi tashin gwauron zabi, wanda ke nuna ƙalubalen tattalin arziki. Bikin sallar da ake yi da yankan dabbobi domin tunawa da yadda Annabi Ibrahim ya yi sadaukarwa da dansa domin Allah, yana zama nauyi ga mutane da yawa a fannin kudi. A kasuwar dabbobi ta Otal ɗin Dubar, farashin Ragunan ya tashi sosai.
Musa Aliyu, mai sayar da Rago, ya bayyana cewa, Ragon da farashinsa ya kai Naira ₦100,000 a shekarar da ta gabata, yanzu yana kai wa ₦200,000 zuwa ₦250,000.
Matsakaitan Raguna, a baya ₦120,000, yanzu suna tsakanin ₦400,000 zuwa ₦600,000. Manyan Raguna, a da suna kan ₦700,000 sun haura zuwa ₦900,000 zuwa Naira miliyan ɗaya. Ana sayar da ƙananan raguna kan Naira ₦70,000 zuwa ₦80,000.
- Idan Mace Ta Yi Barin Cikin Wata Biyu, Za Ta Dakatar Da Yin Sallah?
- Gwamna Radda Ya Amince Da Bai Wa Ma’aikata N15,000 A Matsayin Goron Sallah
Masu sayar da dabbobi irin su Hassan Mohammed sun koka da ƙarancin masu saye da aka samu saboda tsadar rayuwa. Ya ƙara da cewa an samu ƙarin kuɗin ne daga masu kawo dabbobin da kuma tsadar abincinsu, wanda a yanzu farashinsa ya kai Naira ₦20,000 zuwa Naira ₦25,000 idan aka kwatanta da Naira ₦10,000 a baya.
Duk da irin wannan tsadar, wasu masu saye irin su Mohammed Idris, na ganin dole su sayi raguna saboda al’adu da addini, duk kuwa da ƙarancin kudi a hannun mutane.
Mazauna yankin sun bayyana takaicinsu dangane da tashin gwauron zabin dabbobin layyar, saboda fargabar cewa za a jefa iyalai da dama cikin matalauta a bukukuwan Sallah na bana.
Musa Yahaya, ma’aikaci ne mai ‘ya’ya bakwai, ya bayyana irin wahalhalun da ake fuskanta a fannin tattalin arziki. Ya ce hatta kayan masarufi kamar fatun buhu sun yi tsada.
Yahaya ya yi kira ga gwamnati da ta shiga tsakani domin rage wa talakawan Najeriya raɗaɗin tattalin arziƙi, saboda hauhawar farashin kayayyaki na kara sanya rayuwar yau da kullum cikin wahala.