Yau Litinin 10 ga wata, aka cika wata daya da maido da shawarwari tsakanin kasashen Saudiyya da Iran da aka yi a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin. A wata dayan da ya wuce, kusan kowace rana ana samun labarai masu dadi, da sabon ci gaba a yankin Gabas ta Tsakiya, inda aka kara samun sulhu a wannan yanki.
A ranar 8 ga watan kuma, tawagar jami’an diflomasiyyar kasar Saudiyya ta isa birnin Tehran na kasar Iran, inda suka tattauna kan batun da ya shafi sake bude ofisoshin jakadancin Saudiyya a Iran. Kuma tuni ministocin harkokin wajen kasashen biyu suka gana a Beijing, inda suka sanar da farfado da huldar jakadancinsu a hukunce. An kara samun ci gaba wajen kyautata dangantaka tsakanin Saudiyya da Iran, bisa jadawalin shawarwarin da suka gudanar a Beijing, al’amarin da ya shaida sahihancin su wajen samun sulhu.
Akwai abubuwa masu sarkakkiya a yanayin da ake ciki a yankin Gabas ta Tsakiya, kana, samun sulhu ba abu ne mai sauki ba. Kuma matsayin kasar Sin kan wannan batu, wato rashin nuna bangarenci, ko neman cimma muradun kanta, ko kuma kulla zumunta da wasu kasashen da take so kadai, ya samu amincewa daga kasashen dake yankin Gabas ta Tsakiya. Har wa yau, shawarar tabbatar da tsaro a duk fadin duniya da kasar Sin ta bullo da ita, ta samu maraba sosai daga kasashen yankin da ma dukkanin duniya. Hakan ya nuna cewa, abun da kasar Sin ta yi ya dace da makomar yankin Gabas ta Tsakiya, wato samar da zaman lafiya da ci gaba. (Murtala Zhang)