Wa’adin da ƙasurgumin ɗan ta’adda, Bello Turji, ya bai wa mahukuntan Nijeriya ya cika a ranar Talata.
Turji ya yi barazanar cewa idan ba a saki wani surukinsa da aka kama a wani asibiti da ke Shinkafi ba, zai hana mazauna yankunan Shinkafi, Zurmi, da Isa zaman lafiya.
- Ta Leko Ta Koma, An Cire Sunan Olmo Daga Jerin Yan Wasan Laliga
- Bangaren Sin Na Fatan Habaka Ma’anar Al’umma Mai Makomar Bai Daya Ta Sin Da Afirka A Sabon Zamani Tare Da Kasashen Afirka
Wannan barazana ta jefa al’ummomin yankunan cikin tsananin fargaba, inda da yawa daga cikinsu suka tsere daga gidajensu domin tsira da rayukansu.
Tuni wasu suka nemi mafaka a wuraren da suka fi tsaro.
Tsohon gwamnan jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, ya nuna damuwarsa kan yadda irin su Bello Turji ke cin karensu babu babbaka.
Ya ce barin irin waɗannan mutane cikin al’umma ba zai haifar wa gwamnati komai ba face matsala.