Duk wani da ya bayar da lokacinsa wajen samun karin ilimin wata sana’a, to lallai ya dara sauran abokan tafiyarsa a dukkan bangarorin rayuwa.
Wannan kuma yana faruwa ne saboda sabon fasahar da mutum ya kowa na sa ya zama ya kara fadada hanyoyin samun kudin shigarsa, yana kuma sa ya kara samun karbuwa a dukkan bangarori. A wannan zamanin da intanet ya zama wani hanya na samun kudaden shiga ga dukkan wanda ya nemi haka kuma yana son ya karu.
- Sin Za Ta Inganta Zamanintarwa Bisa Bunkasuwa Mai Inganci Don Ba Da Karin Karfi Ga Ci Gaban Duniya
- Ɗiawara Ya Fice Daga Tawagar Faransa Bayan An Hana ‘Yan Wasa Yin Azumi
A wannan lokacin da ma’iakatu da kamfanoni ke kara dogara da ilimin kimiyya da fasaha, samun ilimin kimiyya da fasaha zai kara buda wa mutum karin hanyoyin samun ci gaba a dukkan bangarorin rayuwa.
Idan ka iya samu ingantattun kayan aiki, zaka iya koyon wasu fasahohi masu dama wadanda zaka iya zamar da su kudi a cikin kwana 90.
A wannan lokacin za mu kawo muku wasu sana’o’i 10 da mutum zai iya lakanta ya kuma amfana da su a cikin kwana 10.
- Saye da sayarwa ta intanet
A bayyana yake a wannann lokacin kafafen sadarwa sun zama bangare na rayuwar al’umma. Kusan kowa ka gani yana mu’amala da kafafafen sadarwa na zamani.
Kafafen sadarwa na zamani ya zama wani fage na tallata hajoji musamman ganin yawan masu mu’amala da kafafen sadarwsa a kullum suna kara yawa ne.
Kana iya farawa ta hanyar kokarin sanin ciki da waje harkar sadarwa na zamani, akwai shafuka masu dama na yadda ake koyar da yadda zaka yi amfani da intanet don tallata hajojin ka.
Da zaran ka samu wannan ilimin sai kuma ka tallata kanka don masu bukata yin mu’amala da kai.
- Binciken gano amsoshin matsalar ilimi
Yana da muhimmanci sanin yadda zaka binciko wasu labarai ko al’amarin da za su yi tasiri ga mutanen da suke amfani da intanet ta yadda zaka ci gajiyar kudi da ake samu ta hanyar wallafa abubuwa a intanet. Ta hanyar sanya hankali mutum zai san yadda zai lakanci wannan fasahar a cikin kasa da kwanaki 10 harma ya fara cin gajiyar ilimin da ya samu.
Da zaran ka lakanci yadda zaka yi wannan bincike zaka iya tallata wa mutane harkar don masu bukata su zo su biya ka yi musu aikin bincike da tallafa hajar.
3.Zane-zane na musamman ta intanet
A wannan lokacin da harkar intanet ke jagorantar harkokin yau da kullum na al’umma, sanin ilimin zane-zane ta intanet zai amfanar sosai. In kuma mutum ya lakanci yadda zai yi zane-zane na zamani ta intanet lallai hakan zai taimaka masa samun karin hanyoyin samun kudin shiga don gudanar da harkokin rayuwarsa.
In har ka samu kayan aiki, kamar kwamfuta da kuma manhajar koyarwa ta intanet lallai zaka lakanci gudanar da zane-zane ta intane a cikin kankanin lokaci.
In ka samar da zane-zane masu ban sha’awa nan take zaka samu masu neman ka sayar musu. Za kuma ka shiga zana alamomin kasuwanci (Logo) da sauran alamomi wanda hakan zai samar maka da kudin shiga ba tare da bata lokaci ba.
- Rubuta tsarin gudanar da shirye-shirye
Dukkan wani bayani da ka gani an wallafa a intanet a duniya zaka samu wani ne ya zauna ya yi rubuta na musamman don amfanar al’umma abin da ake kira da (Content creation). ‘Content’ shi ne ginshikin tallata kaya da hajoji da ra’ayoyi a kafar sadarwa ta intanet, a kan haka mallakar wannan ilimi abu ne da zai kara darajar mai ita ya kuma bude masa hanyoyin samun kudin shiga.
- Harkar kasuwanci ta Email
Gudanar da harkokin kasuwanci ta email na daya daga cikin ingantattun hanyoyin da masu harkar kasuwanci za su yi amfani da su wajen tallata kasuwancinsu.
Ta hanyar sanin hanyoyin tallata kasuwanci ta email mutum zai taimaka wajen bunkasa harkokin kasuwancin al’umma masu hulda da shi.
Akwai hanyoyi da manhajoji masu yawa da zai iya baka ilimin sanin hanyoyin amfani da tsarin ‘email marketing’ wajen tallata harkokin kasuwanci.
- Kirkirar manhaja
A halin yanzu sanin yadda zaka kirkiri manjaha ga masu bukata, wata hanya ce da za ta kara bude wa mutum hanyoyin karuwar arziki.
Da zaran ka mallaki wannan ilimi zaka iya taimaka wa masu kamfanonu ko harkokin kaswuanci wajen su mallaki shafi na kansu a intanet, ta yadda suma za a dama da su a fagen intanet a fadin duniya.
Akwai kafafe da dama a intanet da mutum zai iya daukar kwas don sanin makaman wannan ilimi, da zaran mutum kware sai ya ci gaba da cin gajiyarsa da bunkasa hanyoyin samun kudaden shigarsa.
- Tantance bayanai
Samar da cikakken bayanai tare da tantance su yana da muhimmanci a kokarin da ake yi don bunkasa harkar ci gaban kamfanoini da kasuwanci.
Duk wani kamfani da aka samu yana samun bunkasa a wannan zamanin zaka samu yana da cikakken tsari na tantace bayanai don amfaninsa ‘data analysts’.
A kan haka samun ilimin tantance bayanai zai taimaka maka wajen shiga a dama da kai a fagen bunkasa harkokin kasuwanci a kasar nan.
Akwai wurare da dama a kafar intanet da ke koyar da wannan ilimin a cikin kankanin lokaci.
- Editin bidiyo
A yayin da lamarin wallafa bidiyo ke kara bunkasa kafar sadarwa na zamani intanet, samun ilimin yin editin na bidiyo zai zama karin dama ne da daukaka.
Da zaran ka mallaki wannan ilimin, masu shirin wallafa bidiyo a kafar intanet za su nemi taimakon ka, za kuma ka rinka aikin ne ba tare da ka fita zuwa wani wuri ba, don daga cikin dakinka zaka ci gaba da gudanar da aikin ba tare da wani wahala ba.
- Bayar da taimako na musamman ta intanet
Karuwa harkokin kasuwanci ta intanet yana ta kara karuwa hakan ya kara bukatar mutanen da suke da ilimin gudanar da harkokin bunkasa kamfanoni tare da kula wa masu shafin intanet shafin don binkasar harkokin kasuwancin su.
Shu ma a kwai kafafe masu yawa a intanet da suke koyar da wannan ilimin kuma in har mutum ya mayar da hankalinsa ya kuma yi azama ba zai dauki wani lokaci ma zai fahimci yadda zai amfana da wannan ilimin.
- Samar da tsarin karatu a intanet
Sanin yadda za a tallata harkokin kasuwanci ta intanet, shin ne babbar dabarar samun nasarar kasuwanci a wannan zamanin. Musamman sanin yadda zaka isar da sakon ga mutanen da ake bukata a lokacin da ake kuma bukata. Saboda haka sanin ilimin koyar da al’umma yadda za su yi talla ta email da amfani da ‘Google Ads’ da kuma sauran kafafen sadarwsa na zamani wani abu ne da zai taimaka wa mutum kara samun kudaden shiga a harkokinsa na yau da kullum.
A wannan bangaren ma akwai kafafe da dama da mutum zai yi amfani da su wajen sanin makaman aiki a cikin dan kankanin lokaci ba tare da wahala ba.