Ta amfani da wannan tsari, wayarka na iya amsar sakonnin Imel ko tes a yayin da kake Magana da wani.
Sai dai kawai ka gansu sun shigo. Kana iya karbar rubutattun sakonni fiye da daya a lokaci guda.
- Yadda Kwamishinan Lafiya Na Kano Ke Sa Wa Ma’aikata Ido Don Hana Makara
- Tsohon Wakilin LEADERSHIP Ya Zama Shugaban Gidan Rediyon Kano
Hakan ya faru ne saboda tsarin na amfani ne da hanyoyi fiye da daya wajen karba ko aikawa da wadannan sakonni.
Ba ruwansa da layin da kake karbar sakonnin kira na sauti, sam. Sai dai kuma, mu a nan galibi, kamfanonin sadarwarmu na amfani da ita ne kawai don bayar da damar shiga ko mu’amala da fasahar Intanet. Kamfanin sadarwa ta Glomobile da MTN duk suna da wannan tsari na GPRS, amma kamar yadda na zayyana a sama, idan ba wayoyin salula na musamman irinsu Black-berry ba, ba a iya amfani da ita sai wajen shiga Intanet kadai. Amma a sauran kasashe ana amfani da wannan tsari wajen karba da aikawa da sakonnin tes, da sakonnin Imel da kuma yin hira da abokinka ta hanyar gajerun sakonni, wato Instant Chat.
Dangane da nau’in wayar salula, akwai yanayin sadarwa iri uku ta amfani da fasahar GPRS. Akwai wayoyin salula masu karfin karbar kira na sauti ko murya da kuma karba ko aikawa da sakonnin tes, duk a lokaci guda. Ma’ana, kana magana, sannan kana rubuta sakon tes, idan ka gama rubutawa, ka aika dashi nan take, ba tare da layin da kake magana da abokinka ya yanke ba. Wadannan wayoyin salula sune ke martaba na farko,
A sahun wayoyin salula masu amfani da fasahar GPRS, wato Class A kenan. Sai dai kuma basu yadu sosai ba, watakil sai nan gaba. Sai kuma wadanda ke biye dasu, wato Class B, wadanda idan kana amfani da fasahar GPRS, ta amfani da Intanet ko sakonnin tes, sai kira ya shigo, to wayar za ta tsayar da wancan layin da kake karbar sako ko kake mu’amala da Intanet, don bai wa layin da ke karbar kira damar sadar da kai da wanda ke kiranka. Wadannan sune kusan kashi tamanin cikin dari na ire-iren wayoyin da ake amfani dasu a yanzu. Sai nau’i na karshe, wato Classs C, wadanda idan kana son amfani da fasahar GPRS, to dole sai ka shiga cikin wayar, ka saita ta da kanka. Da zarar ka saita ta, to ba wanda zai iya samunka, sai in ka gama abin da kake, ka sake saita ta zuwa layin karbar kira na sauti ko murya (boice call).
Wannan fasahar sadarwa ta GPRS dai na cikin fasahohin da suka kara wa wayar salula tagomashi da kuma karbuwa a duniya. Domin ta sawwake hanyoyin yadawa da kuma karbar sakonni ba tare da mushkila ba.
 Mun zakulo muku ne daga shafin fasahar Sadarwa a Intanet