Assalamu alaikum masu karatu barkammu da sake saduwa da ku a wannan makon a cikin shirin namu mai farin jini da albarka na Girki Adon Mata.
Da fatan mun yi Sallah lafiya Allah ya maimaita mana amin.
- Sabanin Da Ake Samu Wajen Zaben Girki Tsakanin Ma’aurata
- Tsadar ‘Yan Tsaki Da Abincinsu Na Neman Tilasta Dakatar Da Sana’ar
Ga Abubuwan da za ki bukata wajen hada wannan shayi;
Sinamon, kaninfari, Citta, Suga, Tukunya.
Da farko za ki samu Sinamon dinki, ki gyara shi idan manya ne za ki iya dan kakkarya shi ya dawo kanana sannan idan yana da datti za ki iya dan kankare shi sama-sama, idan za ki hada shi za ki wanke shi, sannan ki zuba shi a tukunya, sai ki zuba kanunfari da citta, cittar busasshiya ake amfani da ita ba danya ba sai ki zuba su gaba daya.
Sannan ki sa ruwa dai-dai yadda kike so sai ki dora shi a wuta ya tafasa sosai za ki ga ya koma kalar ruwan kasa haka shi ne ya dahu sai ki zuba a kofi ki sa suga.
Habba uwargida! Gaskiya yana da dadi so sai ga kamshi kuma yana gyara jiki sai kin ga yadda maigida zai yi santi tare da yara musamman ma yanzu da dan sanyin damuna zai yi dadi sosai, sannan kuma yana maganin sanyi sosai kuwa, sai ki zuba sauran a flas idan kuna bukata an jima idan ruwan shayin ya kare kar ki zubar shi za ki iya yi kamar sau biyu zuwa uku kafin ya salamce.